Kishi kumallon mata: Matar aure ta kashe karuwar da ta kama tana soyayya da mijinta

Kishi kumallon mata: Matar aure ta kashe karuwar da ta kama tana soyayya da mijinta

- Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta damke wata matar aure mai suna Ada Amuzie da laifin kisan kai

- Ada dai ta fusata da yadda wata karuwa mai suna Happiness ke dauke hankalin mijinta, lamarin da yasa ta bi ta har gida da wuka wacce ta soka mata

- Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan jihar Imo din ya bayyana, an fara bincike kuma za a gurfanar da wacce ake zargi a gaban koto

Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta damke wata matar aure mai suna Ada Amuzie. Ana zargin Amuzie da halaka wata karuwa mai suna Happiness wacce ta zarga da mu'amala da mijinta mai suna Ejike Lambert Amuzie, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan, Orlando Ikeokwu ya sanar, ya ce a ranar Asabar, 28 ga watan Maris ne Ada ta shiga har gidan Happiness don kalubalantarta amma dauke da wuka. Sa'a ta kubcewa Happiness don kuwa Ada ta fi karfinta kuma sai ta soka mata wukar.

"A ranar 28 ga watan Maris din 2020 ne wajen karfe 11:45 na dare a Imika Obiti da ke karamar hukumar Egbema, jami'an hedkwatar 'yan sandan Ohaji suka samu rahoton kama Ada Amuzie mai shekaru 26 a kan laifin kisan wata karuwa mai suna Happiness.

"Binciken farko ya bayyana cewa Ada Amuzie ta zargi Happiness da soyayya da mijinta mai suna Ejike Lambert. A wannan ranar kuwa matar auren ta bi karuwar har gida inda suka fara fada. Lamarin da yasa ta sokawa karuwar wuka a kasan kirjinta wanda yayi sanadiyyar mutuwarta." Takardar tace.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya kara da cewa, an mika gawar mamaciyar zuwa ma'adanar gawawwaki a asibiti yayin da aka damke wacce ake zargi kuma za a mika ta kotu bayan kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel