Annobar Coronavirus: Ku rage ma yan Najeriya kudin kira da na Data - Sheikh Pantami

Annobar Coronavirus: Ku rage ma yan Najeriya kudin kira da na Data - Sheikh Pantami

A kokarinta na rangwanta ma al’ummar Najeriya bisa mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki sakamakon barkewar annaobar Coronavirus, gwamnatin Najeriya ta nemi kamfanonin sadarwa su sassauta ma yan Najeriya.

Gwamnatin ta bayyana haka ne ta bakin Ministan sadarwa, Sheikh Dakta Isah Ali Pantami, wanda ya bayyana haka a shafinsa na dandalin sadarwar zamani ta Facebook a daren Talata, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Annobar Corona: Aminu Dantata ta bayar da naira miliyan 300 domin yaki da Corona

A cewar Pantami; “A matsayina na ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani wanda ke kula da tsare tsaren masana’antar sadarwa a Najeriya kamar yadda dokar NCA na shekarar 2003 kashi na 1 ta bayyana

“Ina kira ga kamfanin MTNNG, GloNg, AirtelNigeria 9Mobileng da sauransu a kan su rage ma yan Najeriya farashin kira ta waya da farashin Data a wannan lokaci da ake fama da radadin Coronavirus.” Inji shi.

A wani labarin kuma, attajirin jahar Kano, kuma dattijon jahar Kano, Alhaji Aminu Alhassan Dantata ya baya da kyautar naira miliyan 300 ga gwamnatin jahar Kano domin yaki da annobar Coronavirus mai toshe numfashi.

Kwamishinan watsa labaru na jahar, Muhammad Garba ne ya bayyana haka a ranar Litinin, inda yace jim kadan bayan Gwamna Abdullahi Ganduje ya kaddamar da kwamitin tattara kudaden taimakon ne sai jama’a da kamfanoni masu zaman kansu suka fara bayar da gudunmuwarsu.

Sauran wadanda suka bayar da tallafin kudin sun hada da Alhaji Abba Sumaila da ya bayar da kwalayen taliya guda 500, Alhaji Abubakar Dalhatu shugaban kamfanin Al-Amsad Group wanda ya bayar da naira miliyan 5.

Haka zalika kwamishinonin gwamnatin jahar Kano da sauran masu rike da mukaman siyasa sun sadaukar da kashi 50 na albashinsu domin gudanar da wannan muhimmin aiki.

A hannu guda kuma, bankin UBA ta bayar da naira miliyan 28, yayin da Dangote ya yi alkawarin samar da cibiyar killace masu dauke da cutar Coronavirus mai gado 600 a filin wasa na Sani Abacha dake Kano.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel