COVID-19: Zan bada Biliyan 1 a matsayin gudumuwa – Inji Folorunsho Alakija

COVID-19: Zan bada Biliyan 1 a matsayin gudumuwa – Inji Folorunsho Alakija

Attajira Folorunsho Alakija wanda ta zarce sa’a a cikin Matan Nahiyar Afrika ta bayyana cewa za ta bada makudan kudi domin taimakawa yakin annobar Coronavirus.

Madam Folorunsho Alakija ta bayyana cewa za ta ba Najeriya gudumuwar Naira biliyan daya ta hannun kamfanin man ta watau Famfa Oil domin a yaki wannan cuta.

Mai kudin ta yi wannan bayani ne a jawabi da ta fitar a shafinta na Tuwita a Ranar Litinin, 30 ga Watan Maris. Kamfanin Alakija zai taimakawa hukumar NCDC ta kasa.

“Yayin da Duniya ta hada-kai domin maganin tasirin lafiya, tsaro, tattali da zamantakewar da Coronavirus ta kawo, babu shakka mu na ganin lallai mu na fama da wadannan matsaloli a kasashe masu tasowa. Maganin annoba irin wannan ya danganta da irin kokarin da mu ka yi.”

Mai kudin ta kara da cewa: “Mu na ta faman hada kudi domin kauda wannan danyen kalubale da mu ke fuskanta a hanyar da ta ke nuna irin jajircewarmu da halinmu da kuma karfinmu”

KU KARANTA: COVID-19: Gwamnatin Najeriya ta na ba Talakawa tallafin kudi

A dalilin haka Folorunsho Alakija ta yi alkawarin bada Naira biliyan 1 domin yakar cutar. Hukumar da ke takaita yaduwar cuta a kasar za ta samu N250, 000, 000.

N250, 000, 000 za su tafi hannun gwamnatin jihar Legas. Kamfanin man na Alakija ya kuma warewa cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa a Afrika N50, 000, 000.

Wannan Baiwar Allah ta kuma bayyana cewa za ta ba Ma’aikatan lafiya da ke Legas N100, 000, 000. Su ma Ma’aikatan da ke Garin Abuja za su tashi da N100, 000, 000.

A karshe kamfanin na FAMFA zai kashe N245, 000, 000 wajen sayo kayan aikin da ake bukata a asibitoci. Cibiyar Dr. Ameyo Stella Adadevoh za ta samu N5, 000, 0000.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel