Annobar Corona: Aminu Dantata ta bayar da naira miliyan 300 domin yaki da Corona

Annobar Corona: Aminu Dantata ta bayar da naira miliyan 300 domin yaki da Corona

Attajirin jahar Kano, kuma dattijon jahar Kano, Alhaji Aminu Alhassan Dantata ya baya da kyautar naira miliyan 300 ga gwamnatin jahar Kano domin yaki da annobar Coronavirus mai toshe numfashi.

Kwamishinan watsa labaru na jahar, Muhammad Garba ne ya bayyana haka a ranar Litinin, inda yace jim kadan bayan Gwamna Abdullahi Ganduje ya kaddamar da kwamitin tattara kudaden taimakon ne sai jama’a da kamfanoni masu zaman kansu suka fara bayar da gudunmuwarsu.

KU KARANTA: Na bada kyautar albashina na wata 10 domin yaki da Coronavirus – Gwamnan Kwara

Annobar Corona: Aminu Dantata ta bayar da naira miliyan 300 domin yaki da Corona
Dantata tare da Dangote
Asali: Facebook

Sauran wadanda suka bayar da tallafin kudin sun hada da Alhaji Abba Sumaila da ya bayar da kwalayen taliya guda 500, Alhaji Abubakar Dalhatu shugaban kamfanin Al-Amsad Group wanda ya bayar da naira miliyan 5.

Haka zalika kwamishinonin gwamnatin jahar Kano da sauran masu rike da mukaman siyasa sun sadaukar da kashi 50 na albashinsu domin gudanar da wannan muhimmin aiki.

A hannu guda kuma, bankin UBA ta bayar da naira miliyan 28, yayin da Dangote ya yi alkawarin samar da cibiyar killace masu dauke da cutar Coronavirus mai gado 600 a filin wasa na Sani Abacha dake Kano.

Ganduje ya kafa kwamitin tara kudaden ne a karkashin jagorancin shugaban jami’ar Bayero, Farfesa Yahuza Bello, wanda aikinta shi ne lalubo mutane ko kungiyoyin da suke da karfin taimakawa domin su taimaka, tare da lalubo irin kayan tallafin da ake bukata, da kuma irin mutanen da ya kamata su samu tallafin.

Daga karshe sanarwar ta bayyana asusun bankin da jama’a zasu iya bayar da gudunmuwarsu kamar haka sunan asusu: Kano State COVID-19 Support, UBA, lambar asusu: 1022751785. Idan kuma kayan tallafi za’a bayar, ana iya kaiwa gida mai lamba 94, Maganda Road da kuma kamfanin buga takardu ta jahar Kamo dake titin gidan Sarki.

A wani labarin kuma, a ranar Lahadi, 29 ga watan Maris ne gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga al’ummar jahar Kano da su dauki azumi a ranar Litinin domin neman agajin Allah game da annobar Coronavirus mai toshe numfashin dan Adam.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake kaddamar da kwamitin mutane 37 da zasu kula da gidauniyar neman tallafi da gwamnatin jahar ta bude domin kare yaduwar cutar zuwa Kano tare da shawo kanta cikin sauki idan ma ta shiga.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel