Annobar Coronavirus: Gwamnan jahar Adamawa ya kaddamar da dokar ta-baci na kwanaki 14

Annobar Coronavirus: Gwamnan jahar Adamawa ya kaddamar da dokar ta-baci na kwanaki 14

Gwamnan jahar Adamawa, Ahmadu Fintiiri ya sanar da dokar hana shige da fice a jahar na tsawon kwanaki 14 a wani mataki na kare jahar daga annobar cutar Coronavirus mai toshe numfashi.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka a ranar Litinin ta bakin mai magana da yawunsa, Humwashi Wonosikou, inda yace gwamnatin ta dauki matakin mai tsauri ne don kare rayukan jama’a.

KU KARANTA: Ka bani naira biliyan 1 domin na yaki Coronavirus – Gwamnan Anambra ga Buhari

“Gwamnatin jahar Adamawa ta sanya dokar ta-baci a duk fadin jahar na tsawon makonni 2 domin kare yaduwar annobar Coronavirus, dokar za ta fara aiki ne daga tsakar daren Litinin. Haka zalika an hana tafiye tafiye tsakanin jahohi, kuma an rufe iyakar jahar da Kamaru.

“Wannan doka ta shafi zirga zirgan ababen hawa da suka hada da babura da keke napep da kuma motocin Bus a duk fadin jahar.” Inji shi.

Gwamnan ya kara da cewa dalilin kaddamar da wannan doka shi ne sakamakon rikon sakainar kashi da ma’aikatan gwamnatin jahar suka yi ma umarnin gwamnatin da ya nemi ma’aikata daga mataki na 12 zuwa kasa su zauna a gida.

“Yayin da annobar COVID-19 ke cigaba da yaduwa a Najeriya zuwa mutane 111, mun dakatar da duk wasu tarukan jama’a, daga ciki har da kulle duk wasu gidajen rawa da matattarar mashaya giya. Kasuwanni ma an kulle su illa ga masu sayar da kayan abinci da magani, gidajen mai da Bankuna.” Inji shi.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak ya bayyana cewa ya sadaukar da albashinsa na watanni 10 domin ganin an dakatar da yaduwar annobar Coronavirus a Najeriya.

A cikin wannan sanarwa da Gwamna Abdulrahman Abdulrazak ya fitar ya bayyana cewa tun daga lokacin da ya zama gwamnan jahar Kwara ba’a taba biyansa albashi ba, don haka yana bukatar albashin a yanzu domin a kashe su wajen yaki da Corona, duk da cewa ba’a samu bullarta a jaharsa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel