Annobar Coronavirus: Daga ranar Talata babu shiga babu fita a jahar Yobe

Annobar Coronavirus: Daga ranar Talata babu shiga babu fita a jahar Yobe

Gwamnan jahar Yobe, Mai Mala Buni ya bayyana daukan matakin garkame jahar Yobe gaba daya daga ranar Talata, 31 ga watan Maris domin kare yaduwar annobar cutar Coronavirus zuwa jahar.

Punch ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Mamman Mohammed a ranar Lahadi, 29 ga watan Maris, inda yace: “Gwamnan jahar Yobe, Mai Mala Buni ya bada umarnin kulle iyakokin jahar Yobe daga ranar Talata.

KU KARANTA: Ka bani naira biliyan 1 domin na yaki Coronavirus – Gwamnan Anambra ga Buhari

“Gwamnan ya yi haka ne domin kawar da shigowar annobar Coronavirus jahar, biyo bayan samun hauhawar masu dauke da cutar a Najeriya. Gwamnan ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa kariyar da ya baiwa jama’an jahar daga cutar.

“Amma duk da rashin samun bullar cutar a jaharmu, gwamnati ta samar da matakan kare kai ta hanyar kafa sansanonin killace kai tare da kafa kwamitin kula da yaduwar cutar a jahar a karkashin jagorancin mataimakin gwamna Idi Barde Gubana.” Inji shi.

Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jahar su bi shawarwarin likitoci da jami’an kiwon lafiya, kuma su kauce ma shiga turmutsitsin jama’a, sa’annan su yawaita wanke hannuwansu lokaci zuwa lokaci.

Sa’annan ya yi kira ga yan kasuwa su kauce ma muguwar halayyar nan na boye kayan abinci da kuma tsawwala musu kudi domin neman kazamin riba, inda yace hakan zai kara jefa jama’a cikin mawuyacin hali.

Daga karshe gwamnan ya nemi al’ummar jahar su jajirce wajen gudanar da addu’o’i tare da neman taimakon Allah madaukakin Sarki ya kare al’ummar jahar da Najeriya gaba daya.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak ya bayyana cewa ya sadaukar da albashinsa na watanni 10 domin ganin an dakatar da yaduwar annobar Coronavirus a Najeriya.

A cikin wannan sanarwa da Gwamna Abdulrahman Abdulrazak ya fitar ya bayyana cewa tun daga lokacin da ya zama gwamnan jahar Kwara ba’a taba biyansa albashi ba, don haka yana bukatar albashin a yanzu domin a kashe su wajen yaki da Corona, duk da cewa ba’a samu bullarta a jaharsa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel