Siyasa ba da gaba ba: Atiku ya jajanta ma El-Rufai bayan kamuwa da Coronavirus

Siyasa ba da gaba ba: Atiku ya jajanta ma El-Rufai bayan kamuwa da Coronavirus

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya jajanta ma gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai bisa ibtila’in da ya same shin a kamuwa cutar Coronavirus.

Ita dai wannan sabuwar annoba tana toshe numfashin dan Adam ne, kuma a yanzu haka wannan cuta ta kama akalla mutane 111 a Najeriya, tare da kashe mutum 1, a ranar Asabar, 28 ga watan Maris ne El-Rufai ya sanar da ya kamu da cutar.

KU KARANTA: Annobar Corona: Al’ummar jahar Kano sun tashi da azumi domin neman taimakon Allah

Siyasa ba da gaba ba: Atiku ya jajanta ma El-Rufai bayan kamuwa da Coronavirus

Siyasa ba da gaba ba: Atiku ya jajanta ma El-Rufai bayan kamuwa da Coronavirus
Source: Facebook

Sai dai a wata sanawar da Atiku ya fitar a ranar Lahadi, ya jajanta ma gwamnan tare da gwamnan jahar Bauchi, Bala Muhammad, da kuma shugaban hukumar kula da shige da fice, Muhammad Babandede, wanda dukkaninsu sun kamu da cutar.

A cewar Atiku: “Kamuwa da cutar Coronavirus ba mutuwa ba ce, don haka ina jinjina musu biya bayyana harbuwa da cutar da suka yi, za mu iya kawo karshen annobar ta hanyar ilimantar da mutane tare da killace kai da kuma yin gwaji, za mu warke gaba dayanmu.” Inji Atiku.

Ga duk mai bin siyasar Najeriya, ya sani cewa akwai tsatstsamar dangantaka tsakanin Atiku Abubakar da gwamnan jahar Kaduna Nasir El-Rufai tun a zamanin da suka yi aiki tare a gwamnatin shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Sai dai duk da wannan, hakan bai hana Atikun jajanta ma El-Rufai ba bayan sakamakon gwajin da aka gudanar a kansa ya tabbatar da ya kamu da cutar Coronavirus, ko da yake akwai dan Atikun dake dauke da cutar, amma hakan ya nuna alakarsu ta siyasa ba gaba ba ce.

A wani labari kuma, A ranar Lahadi, 29 ga watan Maris ne gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga al’ummar jahar Kano da su dauki azumi a ranar Litinin domin neman agajin Allah game da annobar Coronavirus mai toshe numfashin dan Adam.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake kaddamar da kwamitin mutane 37 da zasu kula da gidauniyar neman tallafi da gwamnatin jahar ta bude domin kare yaduwar cutar zuwa Kano tare da shawo kanta cikin sauki idan ma ta shiga.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel