An sa tukwici don cafke wadanda suka yi garkuwa da yayan gwamnan Bauchi

An sa tukwici don cafke wadanda suka yi garkuwa da yayan gwamnan Bauchi

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya yi alkawarin bayar da kyautan zunzurutun kudi har Naira miliyan 2 a matsayin tukwici ga duk wanda ya bayar da bayannai da su taimaka a ceto dan uwansa da aka sace.

The Nation ta ruwaito cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi awon gaba da yayan gwamnan, Adamu Mohammed.

An ruwaito cewa an sace shi na misalin karfe 7 na yamma a Kobo Streer da ke birnin Bauchi a ranar Laraba 25 ga watan Maris na shekarar 2020.

An sa tukwici don cafke wadanda suka yi garkuwa da dan uwan gwamnan Bauchi
An sa tukwici don cafke wadanda suka yi garkuwa da dan uwan gwamnan Bauchi
Asali: Twitter

Mai bawa gwamna shawara na musamman a kan sabuwar kafar yada labarai, Mukhtar Gidado ne ya bayar da wannan sanarwar tukwicin da za a bawa duk wanda ya bayar da bayyanan da suka taimaka aka ceto yayan gwaman cikin koshin lafiya cikin sakon da ya raba wa manema labarai a Bauchi.

DUBA WANNAN: COVID-19: Fadar shugaban kasa ta karyata jita-jitar cewa za a raba wa 'yan Najeriya N30,000

Sanarwar ta ce, "Iyalan sa za su bayar da kudi Naira Miliyan biyu (N2m) ga duk wanda zai iya bayar da bayyanai da su taimaka a ceto shi."

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa, a ranar Alhamis ta sanar da cewa ta rufe iyakokin ta na kasa da jihar Bauchi da ta ke makwabtaka da ita da wasu jihohin bayan an samu bullar cutar da coronavirus a jihar.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Abba Zakari ne ya shaidawa manema labarai hakan inda ya ce dokar za ta fara aiki daga ranar Juma'a 27 ga watan Maris.

Mista Zakari ya ce jihar ta tuntubi dukkan masu ruwa da tsaki a fanin da suka hada da kungiyar direbobi na kasa (NURTW) domin tabbatar da cewa kowa ya bi dokar.

Mista Zakari wanda shine shugaban kwamitin ta baci da aka kafa domin kare yaduwar Covid-19 a jihar ya ce sauran hanyoyin da aka rufe sun hada da hanyar da ta hada Jigawa da Kano, Yobe da Katsina.

Kwamishinan ya sake jadadda cewa jihar ba za ta amince da taro na mutane da ya dara 20 ba kuma hukumomin tsaro za su sanya ido domin ganin an bi dokan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel