Annobar Corona: Al’ummar jahar Kano sun tashi da azumi domin neman taimakon Allah

Annobar Corona: Al’ummar jahar Kano sun tashi da azumi domin neman taimakon Allah

A ranar Lahadi, 29 ga watan Maris ne gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga al’ummar jahar Kano da su dauki azumi a ranar Litinin domin neman agajin Allah game da annobar Coronavirus mai toshe numfashin dan Adam.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake kaddamar da kwamitin mutane 37 da zasu kula da gidauniyar neman tallafi da gwamnatin jahar ta bude domin kare yaduwar cutar zuwa Kano tare da shawo kanta cikin sauki idan ma ta shiga.

KU KARANTA: Tashin hankali yayin da rundunar Yansanda ta umarci jami’anta su tashi daga bariki

Annobar Corona: Al’ummar jahar Kano sun tashi da azumi domin neman taimakon Allah
Ganduje da Yahuza
Asali: Facebook

“Ina kira ga jama’an Kano su yi azumi a ranar 30 ga watan Maris, wanda ya yi daidai da 5 ga watan Sha’aban kuma su dage da addu’a a kan hana bullar Coronavirus a jaharmu, haka zalika ina kira ga jama’a da mu dage da addu’o’i domin addu’a kadai ita ce mafita.” Inji shi.

Ganduje ya kara da cewa akwai bukatar kafa gidauniya neman tallafin kudi da za ta taimaka ma gajiyayyu da marasa galihu a wannan lokaci da aka rufe ko ina a dalilin wannan annoba.

“Yayin da muke daukan matakan kare yaduwar cutar Coronavirus, akwai wasu rukunin mutane da ba zasu iya cin abinci ba sai sun fita sun nema don kulawa da iyalansu, akwai kuma masu karamin karfi, don haka dukansu suna neman taimako.” Inji shi.

Gwamnan ya ce wannan ne yasa suka kafa kwamitin domin su tara kudi don rage musu radadin kulle da aka musu. Haka zalika ya kara kira ga tsofaffin jami’an kiwon lafiya da suka yi ritaya dasu taimaka su koma bakin aiki na wucin gadi don ganin an yaki annobar tare.

A jawabinsa, shugaban kwamitin, Farfesa Yahuza Bello na jami’an Bayero University Kano, ya bayyana manufarsa na ganin sun cimma manufar kwamitin, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Daga cikin ayyukan kwamitin akwai lalubo mutane ko kungiyoyin da suke da karfin taimakawa domin su taimaka, tare da lalubo irin kayan tallafin da ake bukata, da kuma irin mutanen da ya kamata su samu tallafin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel