Yanzu-yanzu: Mutane 14 sun sake kamuwa da Coronavirus a Najeriya, jimilla 111

Yanzu-yanzu: Mutane 14 sun sake kamuwa da Coronavirus a Najeriya, jimilla 111

Hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karuwar mutane 14 da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya.

Hukumar ta bayyana hakan a shafin raayinta na Tuwita ranar Lahadi inda tace: “An tabbatar da mutane 14 sun kamu da #COVID19 a Najerya. 5 a Abuja, 9 a Legas.“

“Dai-dai Karfe 9:30 na daren 28 ga Maris, mutane 97 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami uku, kuma daya ya rigamu gidan gaskiya.“

Ga jerin jiha-jiha

Lagos- 68

FCT- 21

Oyo- 7

Ogun- 3

Enugu- 2

Edo- 2

Bauchi- 2

Osun-2

Ekiti- 1

Rivers-1

Benue- 1

Kaduna- 1

Yanzu-yanzu: Mutane 14 sun sake kamuwa da Coronavirus a Najeriya, jimilla 111

Yanzu-yanzu: Mutane 14 sun sake kamuwa da Coronavirus a Najeriya, jimilla 111
Source: Twitter

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya dokar hana fita a birnin tarayya Abuja, da kuma jihohin Ogun da Legas, na tsawon makonni biyu domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Ya sanar da hakan ne a jawabin da ya yiwa yan Najerya da yammacin Lahadi, 29 ga Maris, 2020.

A cewarsa, dukkan mazaunan wadannan jihohi su kasance cikin gidajensu kuma su guji tafiya zuwa wata jiha.

Amma ya togaciye wani bangaren mutane da ya hada da yan kasuwa masu sayar da kayan abinci, kamfanonin man fetur, ma-aikatan wutan lantarki da jamian tsaro masu zaman kansu.

Hakazalika kamfanonin sadarwa, da kuma yan jaridan da ba zasu iya aiki daga gida ba.

Yace “Bisa ga shawarar maaikatar kiwon lafiya da hukumar NCDC, ina bada umurnin hana hada-hada a Legas da birnin tarayya na tsawon kwanaki 14 fari daga karfe 11 na dare na ranar Litinin, 30th ga Maris, 2020.“

“Wannan dokar hana fitar za ta shafi jihar Ogun saboda kusancinta da jihar Legas da yawan tafiye-tafiyen da ake tsakaninsu.“

“Lallai mun san wannan mataki zai tsanantawa mutane da dama, amma wannan lamarin rayuwa ko mutuwa ne idan muka lura da irin yadda ake mutuwa kullum a Italiya, Faransa da Andalus.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel