Yanzu-yanzu: Buhari ya sanya dokar ta baci a Abuja, Legas da Ogun

Yanzu-yanzu: Buhari ya sanya dokar ta baci a Abuja, Legas da Ogun

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya dokar hana fita a birnin tarayya Abuja, da kuma jihohin Ogun da Legas, na tsawon makonni biyu domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Ya sanar da hakan ne a jawabin da ya yiwa yan Najerya da yammacin Lahadi, 29 ga Maris, 2020.

A cewarsa, dukkan mazaunan wadannan jihohi su kasance cikin gidajensu kuma su guji tafiya zuwa wata jiha.

Amma ya togaciye wani bangaren mutane da ya hada da yan kasuwa masu sayar da kayan abinci, kamfanonin man fetur, ma-aikatan wutan lantarki da jamian tsaro masu zaman kansu.

Hakazalika kamfanonin sadarwa, da kuma yan jaridan da ba zasu iya aiki daga gida ba.

Yace “Bisa ga shawarar maaikatar kiwon lafiya da hukumar NCDC, ina bada umurnin hana hada-hada a Legas da birnin tarayya na tsawon kwanaki 14 fari daga karfe 11 na dare na ranar Litinin, 30th ga Maris, 2020.“

“Wannan dokar hana fitar za ta shafi jihar Ogun saboda kusancinta da jihar Legas da yawan tafiye-tafiyen da ake tsakaninsu.“

“Lallai mun san wannan mataki zai tsanantawa mutane da dama, amma wannan lamarin rayuwa ko mutuwa ne idan muka lura da irin yadda ake mutuwa kullum a Italiya, Faransa da Andalus.“

Yanzu-yanzu: Buhari ya sanya dokar ta baci a Abuja, Legas da Ogun
Yanzu-yanzu: Buhari ya sanya dokar ta baci a Abuja, Legas da Ogun
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng