COVID-19: Dan majalisa ya yi rabon kayan abinci da kayan afani don tallafawa jama'arsa a Kano

COVID-19: Dan majalisa ya yi rabon kayan abinci da kayan afani don tallafawa jama'arsa a Kano

Wani dan majalisar wakilai mai suna Sha'aban Ibrahim Sharada ya kaddamar da hanyar rage illolin barkewar annobar COVID-19 wacce ta sanya gwamnatin jihar Kano ta rufe iyakokinta.

Sha'aban Ibrahim Sharada dan majalisa ne mai wakiltar mazabar birnin Kano a majalisar wakilai ta kasa. A ranar Lahadi ne ya bayyana kyautatawar da ya shiryawa mazabarsa ga jaridar Solacebase da ke birnn Kano.

Ya ce an raba dubban sinadarin tsaftace hannuwa(hand sanitizer), takunkumin fuska da kuma safunan hannu ga jama'ar Birnin Kano.

Takardar da ya mika ga jaridar Solacebase ta ce, an raba buhunan kayan abinci irinsu shinkafa ga jama'ar da ba za su iya fita nema ba a jihar tunda an rufeta tun a daren Juma'a.

COVID-19: Dan majalisa ya yi rabon kayan abinci da kayan afani don tallafawa jama'arsa a Kano

kayan abinci
Source: Twitter

COVID-19: Dan majalisa ya yi rabon kayan abinci da kayan afani don tallafawa jama'arsa a Kano

Sinadarin tsaftace hannu
Source: Facebook

Dan majalisar ya ce bayan rufe makarantun da aka yi, ya shirya bita a gidan rediyon Dala FM da ke Kano don taimakawa 'yan makaranta masu shirin zana jarabawa kammala sakandire.

"Darasin Turanci da Lissafi za a dinga yi daga ranar Litinin zuwa Asabar, daga karfe 10 na safe zuwa 11.

" Darussan Chemistry da Physics za a dinga yinsu a ranakun Litinin, Laraba da Juma'a daga karfe 11 na safe zuwa 12 na rana.

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta ankarar da jama'a a kan sabon salon damfara da sunan COVID-19

"Darussan Geography da Biology za a dinga yin su a ranakun Talata, Alhamis da Asabar daga karfe 11 na safe zuwa 12 na rana."

Sha'aban Ibrahim Sharada yayi kira ga jama'a da su tsananta addu'a da kuma kiyaye shawarwarin masana kiwon lafiya na wanke hannu da kuma gujewa taruka. Ya shawarci jama'ar jihar, Najeriya da na duniya da su kiyaye hanyoyin yaduwar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel