Gwaji ya nuna ba na dauke da kwayar cutar Coronavirus inji Garba Shehu

Gwaji ya nuna ba na dauke da kwayar cutar Coronavirus inji Garba Shehu

Babban Mai taimakawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya yi magana game da gwajin da ya yi na cutar COVID-19.

Malam Garba Shehu ya bayyana cewa sakamakon gwajin da ya yi ya tabbatar da cewa bai kamu da cutar Coronavirus da a halin yanzu ta zama annoba a Duniya ba.

Hadimin shugaban Najeriyar ya shaidawa Duniya wannan ne ta shafinsa na sada zumunta na Tuwita. Shehu ya bayyana wannan a Ranar 28 ga Watan Maris, 2020.

Ya ce: “Ina tunanin zai yi yi kyau in kwantarwa Abokai da ‘Yanuwa wadanda na yi mu’amala da su ba da dadewa ba hankali game da (kamuwa) da cutar Coronavirus.”

“Kafofin da ke yada labaran karya sun yi ta fadan maganganun banza a game da ni da kuma shugaban kasar (Muhammadu Buhari) da na ke yi wa aiki.” Inji Shehu.

KU KARANTA: Babu maganar rabawa jama'a N30, 000 saboda yaki da COVID-19 Inji Buhari

“Sakamakon gwajina ya tabbatar da cewa ban kamu da kwayar cutar ba. Na godewa Ubangiji. Duk da haka ina bada shawara ga kowa mu cigaba da aiki daga gida.”

Shehu ya yi wannan bayani ne da kimanin karfe 7:45 na Ranar Asabar. Wannan labari ya kwantarwa jama’a hankali, musamman na-kusa da Hadimin na Buhari.

Kwanakin baya ne aka tabbatar da cewa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, ya kamu da cutar. Ofishin Kyari bai da nisa da na Shehu a fadar Aso Villa.

Jim kadan bayan Malam Shehu ya tabbatar da cewa bai kamu da wannan cuta ba, ya kuma yi addu’a ga Ubangiji ya ba Nasir El-Rufai wanda ya kamu da cutar lafiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel