Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 8, jimilla 97

Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 8, jimilla 97

Hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karuwar mutane takwas da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya.

Hukumar ta bayyana hakan a shafin raayinta na Tuwita ranar Asabar inda tace: “An tabbatar da mutane takwas sun kamu da #COVID19 a Najerya. 2 a Abuja, 4 a Oyo, 1 a Kaduna, 1 a Osun.“

“Misalin karfe 10:40 na ranar 28 ga Maris, an samu mutane 97 da aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami uku, kuma daya ya rigamu gidan gaskiya.“

Ge jerin bullar a jihohi

Lagos- 59

FCT- 16

Ogun- 3

Enugu- 2

Ekiti- 1

Oyo- 7

Edo- 2

Bauchi- 2

Osun-2

Rivers-1

Benue- 1

Kaduna- 1

Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 8, jimilla 97

An samu karin masu cutar Coronavirus 8, jimilla 97
Source: Facebook

Mai girma Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya shaidawa Duniya cewa ya na cikin wadanda cutar nan ta COVID-19 ta kama a halin yanzu.

Kwamishinan harkar tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya tabbatar da wannan a shafinsa na Tuwita da kimanin karfe 8:10 na daren Asabar.

Mista Samuel Aruwan ya fitar da cikakken jawabin da Mai girma gwamnan jihar ya yi, bayan ta tabbata ya kamu da wannan cuta ta Coronavirus.

Gwamnan ya bayyana cewa gwajin da ya yi, ya nuna cewa ya na dauke da kwayar COVID-19. Gwamnan ya ce a halin yanzu ya killace kansa.

Sai dai duk da haka ya yi kira ga jama’a su bi dokoki da sharudan da aka gindaya domin hana yaduwar cutar ta Coronavirus da ta addabi kasashe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel