Gwamnatin jihar Plateau ta gargadi Yahaya Jingir

Gwamnatin jihar Plateau ta gargadi Yahaya Jingir

Gwamnatin jihar Plateau a ranar Asabar ta gargadi shugaban kungiyar Jamma’atu Izalatil Bid’a Waikamatis Sunnah, Sheik Sani Yahaya Jingir, kan take dokar gwamnatin jihar na dakatad da Sallar Jumaa saboda yaduwar cutar Coronavirus.

A jawabin da sakataren gwamnatin jihar, Danladu Atu, ya rattafa hannu, ya bayyana cewa gwamnati ba zata lamunci irin wannan halin take doka ba da kan jefa rayukan mutane cikin hadari.

Danladi Atu yace “Gwamnati ba zata lamunci irin wannan halin rashin mutunci na saba doka da wasu mutane da kungiyoyi ke yi ba.“

Za ku tuna cewa a ranar Laraba gwamnan jihar, Samuel Bako Lalong, ya bada umurin kulle dukkan kasuwanni illa masu sayar da kayan abinci da magani.

Amma Sheik Jingir a ranar Juma-a ya ce shi da mabiyansa sun halarci Jumma’a da hujjan cewa tun da babu wanda ya kamu da cutar tukunnan a jihar, babu dalilin da zai sa a daina Sallah.

Ya kara da cewa “Ya tara mabiyansa su saba dokar gwamnati da aka sanya domin kare rayukan alummar. “

“Bari in bayyana karara cewa babu wanda yafi karfin doka kuma gwamnati za ta dau matakin da ya dace. “

Gwamnatin jihar Plateau ta gargadi Yahaya Jingir
Gwamnatin jihar Plateau ta gargadi Yahaya Jingir
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel