COVID-19: An samu karin mutum 8 da suka kamu da cutar a Najeriya, jimilla 89

COVID-19: An samu karin mutum 8 da suka kamu da cutar a Najeriya, jimilla 89

- Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta kara tabbatar da sabbin mutane 8 da suka kamu ta kwayar cutar Covid-19

- Hukumar ta NCDC ta bayyana hakan ne a shafin ta Twitter inda ya ce 7 cikin sabbin masu dauke da cutar a Legas aka samu sai daya a Benue

- Hukumar ta ce kawo yanzu a ranar Asabar 28 ga watan Maris, an tabbatar da mutane 89 ne ke dauke da cutar sannan mutum daya ya mutu

Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta kara tabbatar da sabbin mutane takwas da suka kamu ta kwayar cutar Covid-19 da aka fi sani da coronavirus a kasar.

A cikin wani sako da ta wallafa a shafin ta na Twitter a ranar Asabar 28 ga watan Maris na 2020, hukumar ta ce an samu sabbin mutane 7 ne a jihar Legas sai kuma an samu mutum daya mai cutar a jihar Benue.

Hakan na nuna cewa jimillan mutanen da ke dauke da kwayar cutar a kasar yanzu ya kai 89.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Sakamakon gwajin coronavirus na Adams Oshiomhole ya fito

Wannan na zuwa ne awanni bayan hukumar ta NCDC ta tabbatar da sabbin mutane 5 da suka kamu da cutar ta coronavirus a kasar.

NCDC a sakon da ta wallafa a Twitter a ranar Juma'a, 27 ga watan Maris ta bayyana cewa an sami mutane uku masu dauke da cutar a birnin tarayya Abuja da kuma guda biyu a jihar Oyo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel