Gwamnatin Gombe ta dakatar da biyan sabon albashi na N30,000 saboda coronavirus

Gwamnatin Gombe ta dakatar da biyan sabon albashi na N30,000 saboda coronavirus

- Gwamnatin jihar Gombe ta bayyana cewa ta dakatar da biyan sabon karancin albashin N30,000 a jihar sakamakon barkewar cutar coronavirus a duniya

- Mataimakin gwamnan jihar, wanda ya jagoranci kwamitin tabbatar da biyan sabon karancin albashin, ya ce ma'aikatar kudin jihar za ta sake duba kasafin kudin 2020

- Amma kungiyar kwadago ta kasa tayi kira ga ma'aikata a kan su kwantar da hankulansu don dakatar da biyan sabon karancin albashin na wucin-gadi ne

Gwamnatin jihar Gombe ta dakatar da biyan sabon karancin albashin N30,000 da za ta fara bayan amincewa da tayi a farko. Gwamnatin jihar ta ce za ta biya N18,000 ne sakamakon illar barkewar annobar coronavirus a duniya wanda ya nakasa tattalin arziki.

COVID-19: Gombe ta dakatar da biyan sabon karancin albashi

COVID-19: Gombe ta dakatar da biyan sabon karancin albashi
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Coronavirus: Kotu ta aike da matar da ta yi wa dan sanda tari a fuska zuwa gidan yari

Mataimakin Gwamnan jihar, Manassah Jatau, wanda ya shugabanci kwamitin tabbatar da biyan sabon karancin albashin, ya ce kwamitin hadin guiwar na ci gaba da duba yiwuwar rage albashin duk masu mukaman siyasa a jihar da manyan sakatarorin gwamnatin jihar.

Mataimakin gwamnan ya ce ma'aikatar kudin jihad za ta sake duba kasafin kudin 2020 don rage shi sakamakon farashin danyen man fetur da yayi warwas a duniya.

Ya kara da bayyana cewa gwamnatin ta dau matakan gaggawa wajen rage barna tare da samar da hanyar adana kudi don tabbatar da an yi ayyukan da suka dace a jihar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kungiyar kwadago tayi kira ga ma'aikatan a kan su kwantar da hankulansu don dakatar da sabon karancin albashin a kasar nan na wucin-gadi ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel