Ku bawa masu maganin gargajiya su gwada baiwar su - Shawarar Sarki ga gwamnatin tarayya kan Coronavirus

Ku bawa masu maganin gargajiya su gwada baiwar su - Shawarar Sarki ga gwamnatin tarayya kan Coronavirus

Sarkin Gargajiya na Owerre dake karamar hukumar Nsukka cikin jihar Enugu, Igwe Emeka Ugwu ya shawarci gwamnatin tarayya da ta nemi taimako daga wajen masu maganin gargajiya akan yadda za a kawo karshen annobar Coronavirus a Najeriya

Da yake amsa tambayar da manema labarai suke yi masa akan wayar da kan jama'a kan annobar a karamar hukumar Nsukka da kewaye, Sarkin ya ce nuna halin ko in kula da gwamnatin Najeriya take yi akan masu maganin gargajiya wajen kawo karshen cutar Corona abu ne da zai zama na dana sani.

Ya ce wasu daga cikin masu maganin gargajiya suna da wata baiwa da Allah ya basu ta samar da maganin kowacce cuta.

Igwe Ugwu ya ce:

"Bai kamata gwamnati ta tsaya tana ji tana gani mutane su dinga shan wahala suna mutuwa ba batare da tabi kowacce irin hanya domin kawo karshen wannan cuta ba.

KU KARANTA: Amurka za ta janye mutanen ta baki daya daga Najeriya saboda annobar Coronavirus

"Yayin da gwamnati take jiran masu ilimin kimiyya su nemo mafita akan wannan cuta, kamata yayi a nemi taimakon masu maganin gargajiya da bokaye ko suna da wata hanya. Najeriya mun sha fama da cutar HIV/AIDS, Lassa Fever, Ebola, da sauransu, saboda haka wannan ma zamu kawo karshenta.

"Wasu masu maganin gargajiyar da bokaye suna da baiwar da suke da ita wajen maganin kowacce cuta, saboda haka gwamnati ta sanya su a cikin wannan lamari na neman maganin wannan cuta, saboda magana ce ake ta mutuwa da rayuwa.

Haka kuma Sarkin gargajiyar ya bukaci mutane da kada su tada hankulansu akan yaduwar da cutar take yi a fadin Najeriya, a cewar shi Allah zai kare kowa daga cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel