Likita 1 da Ungozoma 2 sun kamu a Coronavirus a asibiti a Abuja

Likita 1 da Ungozoma 2 sun kamu a Coronavirus a asibiti a Abuja

Sakamakon gwaji ya nuna cewa Likita daya da ungozoma biyu sun kamu da cutar Coronavirus a wani asibiti cikin birnin tarayya Abuja. Sahara Reproters ta ruwaito.

Ma’aikatan kiwon lafiyan sun kasance ma'aikatan wani asibitin gwamnati a Abuja kuam suna cikin ma’aikatan da suka karbi wani mara lafiya da aka kawo asibitin.

Wani babban jami’in asibitin ya bayyanawa manema labarai cewa “An kawo mara lafiyan asibiti kuma kamar da yanayin aikinmu yake, sai mukayi kokarin ceton rayuwar mara lafiyan.”

“Ana gudanar da gwajin akan mara lafiyan sai aka samu cutar Coronavirus ne.”

“Sai asibitin ta bukaci dukkan wadanda suka karbi bakuncin mara lafiyan su yi gwaji domin sanin ko sun kamu, daga karshe an samu cewa uku ma’aikata uku sun kamu.”

“Yanzu haka suna asibitin koyarwan jami’ar Abuja dake Gwagwalada.”

Babban jami’in asibitin ya kara da cewa ma’aikatan asibtin na fama rashin ingantattun kayayyakin kare kai kuma wajibi ne gwamnati ta zuba kudi wajen kare rayukan ma’aikatan kiwon lafiya dake aiki tukuru wajen yakar Coronavirus.

Likita 1 da Ungozoma 2 sun kamu a Coronavirus a asibiti a Abuja
Likita 1 da Ungozoma 2 sun kamu a Coronavirus a asibiti a Abuja
Asali: Facebook

KU KARANTA: Ministocin Buhari 43 sun bada gudunmuwan kashi 50% na albashinsu don yakar Coronavirus– Lai Mohammed

A bangare guda, Kasar Italiya ta waye gari yau Jumaa cikin bakin ciki da radadi sakamakon mutuwar mutane 969 sakamakon cutar Coronavirus, adadi mafi yawa a duniya tun barkewar cutar.

Amma adadin masu kamuwa da cutar ta ragu a yau, yayinda hukumar hana yaduwar cutar kasar ta bayyana cewa kawo yanzu mutane 86,500 suka kamu da cutar - ta biyu bayan kasar Amurka mai sama da 100,000.

Kawo yanzu mutane 558,905 sun kamu da cutar. Yayinda mutane 127,709 sun warke, 25,251 sun rigamu gidan gaskiya.

A ranar Jumaa, an bayyana Amurka matsayin hedkwatar Coronavirus a duniya yayinda ta zarcewa Italiya matsayin kasa mafi yawan masu dauke da cutar.

A nahiyar Afrka kuwa, mutane 3,746 suka kamu da cutar, mutane 192 sun warke kuma 92 sun rigamu gidan gaskiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel