Coronavirus: Kotu ta aike da matar da ta yi wa dan sanda tari a fuska zuwa gidan yari

Coronavirus: Kotu ta aike da matar da ta yi wa dan sanda tari a fuska zuwa gidan yari

Kotu ta daure wata mata a gidan yari bayan ta yi wa wani jami'in dan sanda tari a fuskarsa inda ta ke ikirarin cewa tana dauke da kwayar cutar Covid-19 da aka fi sani da coronavirus.

Joanne Turner, mai shekaru 35 da haihuwa ta fara zagin 'dan sandan ne bayan ta lalata wani mota da aka yi pakin a wajen tashar jiragen kasa na birnin Norwich misalin karfe 11 na daren ranar Laraba.

A kotun majistare da ke Norwich a ranar Alhamis, Turner ta amsa cewa ta ci zarafin wani ma'aikacin bayar da gaggawa a cewar 'yan sandan Norflok.

Coronavirus: Kotu ta aike da matar da ta yi wa dan sanda tari a fuska gidan yari
Coronavirus: Kotu ta aike da matar da ta yi wa dan sanda tari a fuska gidan yari
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: Ba abinda ya shafi jama'a bane - FG ta yi martani a kan lafiyar Abba Kyari

Ta amsa cewa tana cikin maye kuma ta yi dabi'a na rashin da'a da tayar da hankulan al'umma da lalata kaya kamar yadda New Telegraph ta ruwaito.

Rundunar 'yan sanda na Norwich ta ce an yanke wa Turner hukuncin zaman watanni 12 a gidan yari.

Dave Marshall ya ce, "Ba za mu amince da wani cin mutunci ko cin zarafi ga jami'an bayar da taimakon gaggawa a kowanne lokaci. Wannnan hukuncin da aka yanke ya nuna munin yi wa mutane tari a fuska ko kuma razana mutane game da yaduwa da Covid-19."

Rundunar 'yan sandan ta kara da cewa wannan hukuncin da kotu ta yanke zai zama gargadi ga duk wanda ke tunanin aikata laifi irin wannan na yi wa mutane barazana ko razana su yayin wannan lokacin annobar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel