COVID-19: Sabbin mutum 11 sun kamu a Najeriya, jimilla 81

COVID-19: Sabbin mutum 11 sun kamu a Najeriya, jimilla 81

Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya (NCDC) ta kara tabbatar da sabbin mutane 11 da suka kamu ta kwayar cutar Covid-19 wato coronavirus a kasar.

An samu karuwar mutane takwas ne a Legas sannan guda biyu a Enugu sai kuma daya a jihar Edo.

Hakkan na nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar a kasar a halin yanzu ya kai 81.

A cewar hukumar ta NCDC, "an samu sabbin mutane 11 da suka kamu da Covid-19 a Najeriya; 8 a jihar Legas, 2 a Enugu da kuma guda daya a jihar Edo kawo yanzu a ranar 27 ga watan Maris na 2020 misalin karfe 11.55 na dare, jimlar wanda suka kamu da cutar COVID-19 a kasar 81. An sallami mutane 3 sai kuma mutum daya ya mutu."

DUBA WANNAN: COVID-19: 'Yan Najeriya sun bukaci a damke Sheikh Jingir bayan ya ja sallar Juma'a (Bidiyo)

Ya zuwa yanzu kwayar cutar coronavirus ta hallaka mutane fiye da 15,000 a fadin duniya.

Mutum daya ne ya mutu a Najeriya bayan kamuwa da kwayar cutar coronavirus, sannan an sallami mutane biyu da suka warke bayan sun sha magungun a cibiyar da aka killace su, kamar yadda kididdigar NCDC ta nuna.

Yawacin mutanen da aka samu da kwayar cutar corona a Najeriya, 'yan kasa ne da suka dawo daga kasashen ketare, musamman turai.

An tabbatar da samun kwayar cutar a jikin manyan jami'an gwamnati guda uku ciki har da shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin shugaban kasa Abba Kyari da a halin yanzu yana samun kulawa daga likitoci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel