Da duminsa: Zamu kaiwa mutane kayan abinci har gida - Gwamnatin Legas

Da duminsa: Zamu kaiwa mutane kayan abinci har gida - Gwamnatin Legas

Gwamnatin jihar Legas ta shirya bankin kayan masarufi domin rabawa gidaje 200,000 a unguwannin talakawa 377 a jihar Legas domin saukake musu radadin dokar hana fitan da aka sanya domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Mazauna, wadanda zasu fuskanci matsalar rashin abinci zasu samu kayan abinci daga gwamnatin jihar.

Gwamnatin jihar tace "Kwanaki bayan gwamnatin Legas ta bada umurnin zama a gida domin takaita yaduwar cutar Coronavirus, gwamnan Babajide Sanwoolu ya shirya wani shirin rage radadi kan talakawan jihar."

Ba tare da bata lokaci ba, Gwamnan jihar, Babajide Sanwoolu, da kansa ya bayyana hakan ne ranar Jumaa a hirar da yayi da manema labarai inda yace

"Ina farin cikin sanar da shirin tattalin arziki ga mazaunanmu domin saukake radadin dokar zaman gida domin takaita yaduwar cutar #COVID19."

"A karon farko, muna sa ran rabawa gidaje 200,000 masu adadin iyalai da ya kai shida. Zamu kara yawan ba tare da bata lokaci ba."

Da duminsa: Zamu kaiwa mutane kayan abinci har gida - Gwamnatin Legas
Gwamnatin Legas
Asali: Facebook

KU KARANTA Mutane 5 sun sake kamuwa da Coronavirus, 3 a Abuja, 2 a Oyo - 70 jimilla

Da duminsa: Zamu kaiwa mutane kayan abinci har gida - Gwamnatin Legas
Gwamnatin Legas
Asali: Facebook

A jiya, Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ta sayi kayan masarufi domin rabawa mutan jihar domin kawar da yunwa yayinda suka zaune a gidajensu bisa dokar ta bacin da aka sanya.

Mataimakiyar gwamnan, Hadiza Balarabe, wacce ta sanar da hakan ranar Alhamis ta ce sun yanke wannan shawara dubi ga irin halin da mutane zasu shiga.

A cewarta, kwamiti na musamman kan yakar cutar ta gana domin tattauna yadda cutar ke cin rayuka sauran jihohi da kasashen waje.

Tace: "Kamar yadda muka bayyana a jawaban da mukayi a baya, gwamnati tana sayen kayan abinci da sauran kayan masarufi domin sauwakewa mutane wahalan zaman gida."

"Za'a raba wadannan kayayyaki cikin unguwanni ta hanyar kananan hukumomi. Wannan aikin kowace al'umma ne saboda mutan unguwa za'a zaba domin rabawa mutanensu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng