Coronavirus: Mutane 969 suka mutu yau a kasar Italiya

Coronavirus: Mutane 969 suka mutu yau a kasar Italiya

Kasar Italiya ta waye gari yau Jumaa cikin bakin ciki da radadi sakamakon mutuwar mutane 969 sakamakon cutar Coronavirus, adadi mafi yawa a duniya tun barkewar cutar.

Amma adadin masu kamuwa da cutar ta ragu a yau, yayinda hukumar hana yaduwar cutar kasar ta bayyana cewa kawo yanzu mutane 86,500 suka kamu da cutar - ta biyu bayan kasar Amurka mai sama da 100,000.

Kawo yanzu mutane 558,905 sun kamu da cutar. Yayinda mutane 127,709 sun warke, 25,251 sun rigamu gidan gaskiya.

A ranar Jumaa, an bayyana Amurka matsayin hedkwatar Coronavirus a duniya yayinda ta zarcewa Italiya matsayin kasa mafi yawan masu dauke da cutar.

A nahiyar Afrka kuwa, mutane 3,746 suka kamu da cutar, mutane 192 sun warke kuma 92 sun rigamu gidan gaskiya.

Coronavirus: Mutane 969 suka mutu yau a kasar Italiya
Coronavirus: Mutane 969 suka mutu yau a kasar Italiya
Asali: Facebook

DUBA NAN Yanzu-yanzu: Mutane 5 sun sake kamuwa da Coronavirus, 3 a Abuja, 2 a Oyo - 70 jimilla

A Najerya kuwa, gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa tana hasashen a kalla mutane 39,000 a jihar za su kamu da kwayar cutar COVID-19 da aka fi sani da coronavirus.

Kwamishinan lafiyar jihar, Farfesa Akin Abayomi, ya bayyana hakan ga manema labarai a ma'aikatar lafiyar jihar da ke Alausa.

Abayomi ya ce, "A hasashen mu muna zaton karshen mummunan lamarin da zamu samu shine mutane 39,000 na jihar Legas su bayyana dauke da cutar."

Ya kara da bayyana cewa, idan kowa ya dinga nisantar shiga jama'a, akwai yuwuwar ya ragu ya kai 13,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel