COVID-19: Ba abinda ya shafi jama'a bane - FG ta yi martani a kan lafiyar Abba Kyari

COVID-19: Ba abinda ya shafi jama'a bane - FG ta yi martani a kan lafiyar Abba Kyari

Gwamnatin tarayyar Najeriya a ranar Alhamis ta ki yin magana a kan halin da shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa, Abba Kyari ya ke ciki bayan sakamakon gwaji ya nuna cewa yana dauke da kwayar cutar Covid-19.

Ministocin gwamnatin Najeriya biyu sun ki cewa komai game da halin da ya ke ciki a yanzu, Ministan Lafiya, Osagie Ehanire da Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed a lokacin da manema labarai suka musu tambayoyi.

Sunce wannan ba batu bane da ya shafi jama'a kamar yadda kowa na da damar ya bar wa kansa batun lafiyarsa.

COVID-19: Ba abinda ya shafi jama'a bane - FG ta yi martani a kan lafiyar Abba Kyari

COVID-19: Ba abinda ya shafi jama'a bane - FG ta yi martani a kan lafiyar Abba Kyari
Source: Twitter

A mabanbantan taron manema labarai da suka gudanar a jiya a Abuja, sun lissafa sunayen ministoci da manyan ma'aikatan fadar shugaban kasa ciki har da Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo da Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha wadanda duk ba su kamu da cutar ba.

DUBA WANNAN: COVID-19: Mu sadaukar da albashinmu na watan Maris - Dan majalisar wakilai

Da ya ke amsa tambayar da aka masa game da halin da hadimin shugaban kasar ya ke ciki, Ministan Lafiyar ya ce: "Ba zan iya fada muku dukkan wadanda suka yi gwaji da sakamakon gwajin ba domin batu ne da ya shafe su su kadai. Amma suna da damar su fada muku da kansu idan sun so."

Mohammed ya ce ba zai iya yin wani bayyani kan lafiyar Kyari ba inda ya ce gwamnati ba za ta iya bayyana halin lafiya da wani ke ciki ba saboda batu ne na sirri.

Ya kara da cewa yana juyayin yadda al'umma ba su fahimta cewa batun lafiya ba lamari bane da ake shelar ta. Ya ce ba shi da ikon bayyana halin lafiyar kowa domin shima kansa a jiya sakamakonsa kawai aka nuna masa saboda haka bai ga na sauran mutanen da suka yi gwaji ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel