Annobar Corona: Ba zamu dage zaben kananan hukumomi ba – ODIEC

Annobar Corona: Ba zamu dage zaben kananan hukumomi ba – ODIEC

Hukumar shirya zabukan kananan hukumomi ta jahar Ondo, ODIEC ta bayyana cewa babu gudu babu ja da baya game da gudanar da zabukan kananan hukumomin da ta shirya yi, duk kuwa da yaduwar annobar Coronavirus da ake samu.

Punch ta ruwaito kwamishinan hukumar mai kula da watsa labaru, Rotimi Olrunfemi ne ya bayyana haka a garin AKure, inda yace hukumar ta sanya matakan kariya domin tabbatar da nasarar zaben.

KU KARANTA: Yan ta’addan Boko Haram sun ji a jikinsu yayin da Sojoji suka daka musu wawa a Borno

Sai dai a hannu guda kuma gwamnatin jahar Ondo ta sanar da dakatar da duk wasu taruka, ciki har da na siyasa don kauce ma yada cutar Coronavirus a tsakanin jama’an jahar, inda a yanzu haka gwamnan jahar, Rotimi Akeredolu ya shiga halwa don killace kansa.

Hukumar ODIEC ta sanya ranar 18 ga watan Afrilu na shekarar 2020 ne a matsayin ranar da zata gudanar da zaben shuwagabannin kananan hukumomi da na kansilolinsu, don haka Rotimi yace sun tanadi matakan da jami’ansu zasu bi domin tabbatar da basu yada cutar ba.

“Hukumar ta sayo sinadarin wanke hannuwa, robobin ruwan wanke hannuwa da sauran kayan aiki wanda tuni ta aikasu ga ofisoshinta dake kananan hukumomi 18 na jahar, za’a samar da kayan a kowanne rumfar akwatin zabe don wanke hannu a ranar.

“Haka zalika zamu takaita taruwan jama’a a wuri daya a ranar zaben a kowanne rumfar zabe da kuma wajen tattara sakamakon zabe, duk don rage yaduwar cutar a Najeriya.” Inji shi.

Daga karshe yace zasu baiwa jami’an hukumar safar hannu domin su kare kansu, kuma zasu yi aiki tare da ma’aikatar kiwon lafiya ta jahar don tabbatar da lafiyan jama’a tare da dakile cutar.

A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Katsina ta sanar da daukan matakin dakatar da sallar Juma’a tare da tarukan bautan mabiya addinin kirista a coci coci, a wani mataki na kandagarki domin kauce ma yaduwar annobar cutar nan mai toshe numfashin dan Adam, Coronavirus.

Kwamishinan watsa labaru na jahar, Abdulkarim Sirikam ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya raba ma manema labaru a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris inda yace duk wani taron daurin aure ko na siyasa sun haramta a wannan lokaci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel