Ba sani ba sabo: Annobar Corona ta harbi shugaban kasar Birtaniya

Ba sani ba sabo: Annobar Corona ta harbi shugaban kasar Birtaniya

Sakamakon gwajin da aka gudanar a kan Firai ministan kasar Birtaniyar, Boris Johnson game da annobar cutar Coronavirus, ta nuna shi ma ya kamu da kwayar da cutar, kamar yadda jaridar Royal Central ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yanzu haka Mista Boris yana can a killace a fadar shugaban kasar Birtaniya dake Lamba 10, Downing Street, inda ake sa ran zai farfado daga mugunyar cutar.

KU KARANTA: Yan ta’addan Boko Haram sun ji a jikinsu yayin da Sojoji suka daka musu wawa a Borno

Ba sani ba sabo: Annobar Corona ta harbi shugaban kasar Birtaniya
Ba sani ba sabo: Annobar Corona ta harbi shugaban kasar Birtaniya
Asali: Facebook

Haka zalika baya ga Johnson, an kebance sauran ma’aikatan fadar gwamnatin Birtaniyan, kamar yadda mai magana da yawun fadar ya bayyana inda aka ruwaito shi yana cewa:

“Bayan fama da wasu kananan alamomin cutar a jiya, Firai minista ya yi gwajin Coronavirus kamar yadda babban likitan Ingila, Farfesa Chris Whitty ya bayyana.

“A fadar gwamnatin aka gudanar da gwajin, kuma sakamakon gwajin ya nuna Firai ministan yana dauke da cutar, saboda haka a yanzu Firai minista ya killance kansa a fadar gwamnatin kasar, amma zai cigaba da jagorantar kokarin da kasar take dauka na yaki da annobar.”

A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Katsina ta sanar da daukan matakin dakatar da sallar Juma’a tare da tarukan bautan mabiya addinin kirista a coci coci, a wani mataki na kandagarki domin kauce ma yaduwar annobar cutar nan mai toshe numfashin dan Adam, Coronavirus.

Kwamishinan watsa labaru na jahar, Abdulkarim Sirikam ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya raba ma manema labaru a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris inda yace duk wani taron daurin aure ko na siyasa sun haramta a wannan lokaci.

Don haka yace gwamnati na shawartar jama’a su takaita ire iren tarukan nan kamar yadda hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC, ta umarta duba da yadda cutar Coonavirus ke cigaba da yaduwa a kasar.

“Haka zalika gwamnati na kira ga jama’a su yi biyayya ga wannan sabon umarni, sa’annan su cigaba da yi ma kasa addua game da wannan mugunyar jarabawa da duniya ke fama da ita.” Inji kwamishina Abdulkarim.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel