Yanzu-yanzu: Kotun koli ta yi watsi da bukatar sake duba shari'ar jihar Zamfara
Labari da duminsa: Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da bukatar da aka shigar na sake duba shari'ar kujerar gwamna, yan majalisar dokokin tarayya da na jiha a jihar Zamfara.
Bugu da kari, kotun ta umurci wadanda suka shigar da bukatar su biya tarar miliyan biyu ga wadanda suka shigar.
Kotun Kolin Najeriya ta fara sauraron bukatar sake duba shariar zaben gwamnan jihar Zamfara da bangaren AbdulAziz Yari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da bangaren suka shigar kan bangaren Sanata Kabiru Marafa a ranar 18 ga Febrairu, 2020.
Bangaren Yari ta jamiyyar APC a jihar Zamfara ta bukaci kotun ta sake duba hukuncin fitittikan dukkan wadanda aka zabe karkashin lemarta a zaben 2019.
Jamiyyar APC a jihar ta shigar da kara ne ta lauyanta, Robert Clarke, inda ta bukaci kotun ta sake duba hukuncin da ta sake ranar 24 ga Mayu, 2019 na sallamar dukkan wadanda suka lashe zabe karkashin APC saboda basu gudanar da zaben fidda gwani ba.

Asali: UGC
Za ku tuna cewa ana saura kwanaki biyar rantsar da sabon gwamnan jihar Zamfara, kwamitin Alkalan kotun koli biyar karkashin CJN Tanko Muhammad sun yi ittifakin cewa jamiyyar APC bata gudanar da zaben fidda gwani ba bisa ga dokokin jamiyyar saboda haka dukkan kuriun da APC ta samu a zaben ya zama banza.
Sakamakon haka, wanda ya zo na biyu a zaben, Bello Matawalle na PDP ya zama zakaran zabe kuma a ranstar da shi matsayin zababben gwamnan jihar Zamfara.
Kotun ta yake hukuncin ne saboda jam'iyyar APC ta gaza gudanar da zaben fidda gwanin cikin 'yayanta gabanin zabe.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng