Coronavirus: An fitar da sakamakon gwajin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha

Coronavirus: An fitar da sakamakon gwajin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha

Sakamakon gwajin kwayar cutar coronavirus da ka aka yi wa sakataren gwamnatin tarayya, SGF, Boss Mustapha da Ministan Lafiya, da babban sakataren ma'aikatan lafiya ta tarayya, Mista Abdullahi Mashi duk ya nuna cewa ba su dauke da kwayar cutar.

Ministan Lafiya na kasa, Dakta Osagie Ehanire ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a babban birnin tarayya Abuja yayin taron manema labarai da aka gudanar domin sanar da al'umma halin da ake ciki game da cutar.

Ministan ya jadadda cewa ba zai iya bayyana sakamakon gwajin kowa ba har sai wanda aka yi wa gwajin ya bayar da izinin yin hakan. Sai dai ya bayyana cewa sakataren gwamnatin na tarayya da sakataren dindindin na ma'aikatar sun bashi izinin ya bayyana sakamakon gwajin na su.

Coronavirus: An fitar da sakamakon gwajin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha

Coronavirus: An fitar da sakamakon gwajin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha
Source: UGC

DUBA WANNAN: Ba a tabbatar cewa Chloroquine na maganin Coronavirus ba - NCDC

A cewarsa, "Na yi gwajin nawa kuma ba na dauke da kwayar cutar. Sakataren na dindindin na ma'aikatan mu shima ya yi nasa kuma baya dauke da kwayar cutar. Shima sakataren gwamnatin tarayya ya bani izinin in bayyana sakamakon gwajin sa, shima baya dauke da shi."

A wani rahoton, mun kawo muku cewa ministan Lafiya na Najeriya, Osagie Ehanire ya ce akwai yiwuwar za a iya yada kwayar cutar Covid-19 da aka fi sani da Coronavirus ta hanyar jima'i.

Yayin jawabin da ya yi wa manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, Mista Ehanire ya ce ya yi imanin cewa "idan mutum yana dauke da kwayar cutar ta coronavirsu, zai iya yada wa ta hanyar jima'i."

Sai dai a akwai bukatar da ayi amfani da kimiyya wurin gwaji domin tabbatar da hakan duba da cewa Covid-19 sabon cuta ne kuma har yanzu ana cigaba da bincike domin gano hanyoyin yaduwar cutar.

Wasu masu binciken kimiyya sun yi ikirarin cewa ba za a iya yada kwayar cutar da hanyar jima'i ba sai dai kawai ta bakin mutum.

Wani mai binciken kimiyya, Jessica Justman da ta yi magana da jaridar Gauradian UK, ya ce a halin yanzu ba su ganin alamun cewa ana iya yada kwayar cutar da hanyar jima'i.

Amma duk da hakan, ta bayar da shawarar idan daya daga cikin ma'aurata ko masoya ya kamu da cutar, zai fi dacewa a kaurace masa domin gudun kamuwa da cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel