Covid-19: Jigawa ta rufe iyakakokin ta da Bauchi, Kano da wasu jihohi biyu

Covid-19: Jigawa ta rufe iyakakokin ta da Bauchi, Kano da wasu jihohi biyu

Gwamnatin jihar Jigawa, a ranar Alhamis ta sanar da cewa ta rufe iyakokin ta na kasa da jihar Bauchi da ta ke makwabtaka da ita da wasu jihohin bayan an samu bullar cutar da coronavirus a jihar.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Abba Zakari ne ya shaidawa manema labarai hakan inda ya ce dokar za ta fara aiki daga ranar Juma'a 27 ga watan Maris.

Mista Zakari ya ce jihar ta tuntubi dukkan masu ruwa da tsaki a fanin da suka hada da kungiyar direbobi na kasa (NURTW) domin tabbatar da cewa kowa ya bi dokar.

Coronavirus: Gwamnatin Jigawa ta rufe iyakar ta da Bauchi, Kano da wasu jihohi biyu

Coronavirus: Gwamnatin Jigawa ta rufe iyakar ta da Bauchi, Kano da wasu jihohi biyu
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Coronavirus: Karya ne, ba a saka wa Buhari na'urar taimakawa numfashi ba - FG

Mista Zakari ya ce, "Daukan wannan matakin ya zama dole duba da yadda annobar ke yaduwa, tuni jihar Kano ta rufe iyakokin ta da wasu jihohi saboda haka ya zama dole Jigawa ita ma ta yi hakan."

Mista Zakari wanda shine shugaban kwamitin ta baci da aka kafa domin kare yaduwar Covid-19 a jihar ya ce sauran hanyoyin da aka rufe sun hada da hanyar da ta hada Jigawa da Kano, Yobe da Katsina.

Kwamishinan ya sake jadadda cewa jihar ba za ta amince da taro na mutane da ya dara 20 ba kuma hukumomin tsaro za su sanya ido domin ganin an bi dokan.

Jami'in ya kuma ce, "Duk da cewa a halin yanzu ba samu bullar cutar a jihar ba, ba za mu so mu ga wani daga cikin mutanen jihar mu ya kamu da cutar ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel