Za mu rabawa mutane kayan abinci a gidajensu - Gwamnatin Kaduna bayan sanya dokar ta baci

Za mu rabawa mutane kayan abinci a gidajensu - Gwamnatin Kaduna bayan sanya dokar ta baci

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ta sayi kayan masarufi domin rabawa mutan jihar domin kawar da yunwa yayinda suka zaune a gidajensu bisa dokar ta bacin da aka sanya.

Mataimakiyar gwamnan, Hadiza Balarabe, wacce ta sanar da hakan ranar Alhamis ta ce sun yanke wannan shawara dubi ga irin halin da mutane zasu shiga.

A cewarta, kwamiti na musamman kan yakar cutar ta gana domin tattauna yadda cutar ke cin rayuka sauran jihohi da kasashen waje.

Tace: "Kamar yadda muka bayyana a jawaban da mukayi a baya, gwamnati tana sayen kayan abinci da sauran kayan masarufi domin sauwakewa mutane wahalan zaman gida."

"Za'a raba wadannan kayayyaki cikin unguwanni ta hanyar kananan hukumomi. Wannan aikin kowace al'umma ne saboda mutan unguwa za'a zaba domin rabawa mutanensu."

Za mu rabawa mutane kayan abinci a gidajensu - Gwamnatin Kaduna bayan sanya dokar ta baci
Gwamnatin Kaduna bayan sanya dokar ta baci
Asali: UGC

DUBA NAN Za mu feshe jihar Legas gaba daya - Gwamna Sanwoolu (Hotuna)

Mun kawo muku labarin cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar ta baci a fadin jihar saboda mutane sun sabawa dokokin farko da gwamnatin ta sanya domin hana shigowa da yaduwar cutar Coronavirus jihar.

Mataimakiyar gwamnan, Hadiza Balarabe, wacce ta sanar da hakan ranar Alhamis ta ce wannan shawara da aka yanke ya yi muwafaqa da kudin tsarin mulkin Najeriya.

A cewarta, kwamiti na musamman kan yakar cutar ta gana domin tattauna yadda cutar ke cin rayuka sauran jihohi da kasashen waje.

Tace: "Kwamitin ta samu rahoton cewa mutane sun sabawa dokokin hana taro a sanarwa daban-daban da tayi cikin kwanaki bakwai da suka wuce."

"An samu rahotonnin mutane sun yi ko oho da dokar hana hawa babur, Keken 'a daidaita sahu' , da motoci fiye da fasinjoji biyu a kujera da aka sanya."

"Saboda haka, daga daren Alhamis, 26 ga Maris 2020, wajibi ne dukkan mazauna jihar Kaduna su zauna a gida . Babu zuwa aiki, babu kasuwanci, babu zuwa wuraren ibada."

"Mutanen da aka amincewa fitowa kadai sune jami'an kwana-kwana, jami'an kiwon lafiya da jami'an tsaro."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel