Yanzu-yanzu: Mutum 1 na kusa da gwamnan Bauchi sun kamu da cutar Coronavirus

Yanzu-yanzu: Mutum 1 na kusa da gwamnan Bauchi sun kamu da cutar Coronavirus

Mutum daya ya sake kamuwa da cutar Coronavirus a Bauchin Yakubu. Kwamishanan kiwon lafiyan jihar, Dakta Aliyu Maigoro, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Alhamis.

Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa mutane 48 da suka hadu da gwamna Bala Abdulkadir sun killace kansu.

An wajabta musu killace kansu na tsawon kwanaki 14 ne domin sanin ko sun kamu da cutar.

Kwamishanan yace daga cikin mutane 48 a akayiwa gwaji, sakamakon 38 ya fito kuma daya kadai ya kamu.

Ya ce wanda ya kamu dan shekara 62 ne.

KU KARANTA: Za mu rabawa mutane kayan abinci a gidajensu - Gwamnatin Kaduna bayan sanya dokar ta baci

Maigoro ya yi kira ga masu hannu da shuni a jihar su taimakawa gwamnati wajen dakile cutar.

Yace: "Muna kira ga masu hannu da shuni da kuma abokan arziki su taimakawa jihar wajen dakile wannan cuta da kayayyakin aiki da magunguna."

A karshe, Maigoro ya ce gwamnatin jihar ta zabi Asibitin Bayara matsayin daya daga cikin wuraren da za'a yi jinyar wadanda suka kamu da cutar.

Za ku tuna cewa gwamnan jihar, Bala AbdulKadir Mohammed, ya kamu da cutar bayan zama cikin jirgi tare da dan tsohon mataimakin shugaban kasa, Mohammed Atiku Abubakar, ya fara kasuwa.

Yanzu-yanzu: Mutum 1 na kusa da gwamnan Bauchi sun kamu da cutar Coronavirus

Coronavirus
Source: UGC

Hukumar hana yaduwar cutuka ta Najeriya wato NCDC, ta bayyana cewa an sake samun karin mutane goma sha hudu da suka kamu da cutar coronavirus a kasar.

A wani jawabi da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris da daddare, hukumar ta ce mutane 12 daga cikinsu a Lagos suke yayin da sauran biyu kuma suke Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel