Ku tayani da addu'a: Matashiya 'yar kwalisa ta fadi yadda take ji bayan kamuwa da coronavirus

Ku tayani da addu'a: Matashiya 'yar kwalisa ta fadi yadda take ji bayan kamuwa da coronavirus

- Wata matashiya 'yar kwalisa, Precious Williams, da aka samu da kwayar cutar coronavirus ta bayyana halin da take ciki

- Ta bayyana cutar coronavirus a matsayin mugun ciwo da bai kamata jama'a su dauke shi da wasa ba

- Matashiyar ta roki masoyanta su tayata da addu'a domin ta samu lafiya

Wata matashiya mai suna Precious Williams ta bayyana mawuyacin halin da take ciki bayan kamuwa da kwayar cutar coronavirus.

Precious ta sanar da cewa an tabbatar ta kamu da kwayar cutar coronavirus a shafinta na dandalin sada zumunta tare da rokon abokanta su tayata da addu'a.

Bayan shafe tsawon sati guda a asibiti, Precious ta bayyana kwayar cutar coronavirus a matsayin "muguwar cuta".

Ta bayyana cewa da kyar take numfashi saboda lahanin da kwayar cutar ta yi wa hunhunta.

"Sakamakon gwaji ya nuna cewa ina dauke da kyawar cutar coronavirus. Ina jin jiki sosai a cikin sati guda da na yi a asibiti. Wannan cuta muguwa ce, ban taba shan azaba kamar yadda nake ji ba yanzu duk lokacin da zan yi numfashi. Ba wasa bane, jama'a ku tayani da addu'a, " kamar yadda Precious ta bayyana.

Ya zuwa yanzu kwayar cutar coronavirus ta hallaka mutane fiye da 15,000 a fadin duniya, sannan kuma tana cigaba da mamaya a sassan duniya.

DUBA WANNAN: Sabbin mutum 5 sun kamu da coronavirus, jimilla 51, ta shiga karin sabbin jihohi 2

Mutum daya ne ya mutu a Najeriya bayan kamuwa da kwayar cutar coronavirus, amma adadin masu dauke da cutar ya haura mutum 50 kuma zai iya karuwa, kamar yadda kididdigar da aka yi a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris, ta nuna.

Yawacin mutanen da aka samu suna dauke da kwayar cutar corona a Najeriya, 'yan kasa ne da suka dawo daga kasashen ketare, musamman turai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel