COVID-19: Sakamakon gwajin ministar FCT ya fito

COVID-19: Sakamakon gwajin ministar FCT ya fito

- Ramatu Aliyu, karamar ministar birnin tarayya, ta bayyana cewa sakamakon gwajinta na COVID-19 ya bayyana kuma bata dauke da cutar

- Ramatu Aliyu ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a ranar Alhamis a yayin da take godiya ga Ubangiji a kan rahamarsa

- Ministan ta ce wannan hukuncin na killace kanta ya biyo bayan rashin son saka rayukan abokan aikinta, hadimanta da sauran jama'a a garari

Ramatu Aliyu, karamar ministar birnin tarayya, ta bayyana cewa sakamakon gwajinta na COVID-19 ya bayyana kuma bata dauke da cutar. Aliyu ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a ranar Alhamis.

A ranar Talata ne ta bayyana cewa ta killace kanta bayyana ta yi mu'amala da wanda aka gane yana dauke da cutar COVID-19 daga bisani.

Ministan ta ce wannan hukuncin na killace kanta ya biyo bayan rashin son saka rayukan abokan aikinta, hadimanta da sauran jama'a a garari.

Ta yi kira ga 'yan Najeriya da su kwantar da hankulansu, yayin da take shawartarsu da daukar dukkan matakan kiyaye yaduwar muguwar cutar, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

"Ina matukar farin cikin sanar da 'yan uwa, abokai, abokan aiki da kuma jama'a babban birnin tarayya cewa bana dauke da cutar COVID-19. Ina godiya ga Allah da ya bani lafiya da kuma ni'imominsa marasa karewa a kaina a wannan lokacin jarabawar," Aliyu ta rubuta.

COVID-19: Sakamakon gwajin ministar FCT ya fito

COVID-19: Sakamakon gwajin ministar FCT ya fito
Source: UGC

KU KARANTA: Covid-19: Hotunan cibiyar killace masu jinyar cutuka masu yaduwa a Kano

"Ina ci gaba da jan hankulanku da ku dauka dukkan matakan kariya daga cutar nan ba don ku kadai ba, har don masoyanku. Kada ku tsorata, za mu fito daga wannan jarabawar da karfinmu. Mu zama lafiya kuma cikin koshin lafiya." ta ce.

Kamar yadda rahoton duniya dangane da cutar ya bayyana, mutane 491,280 ne suka kamu da cutar a fadin duniya. An samu mutuwar mutane 22,166 inda mutane 118,060 suka warke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel