Yanzu-yanzu: Sakamakon gwajin Coronavirus da aka yi wa Lai Mohammed da Akeredolu ya fito

Yanzu-yanzu: Sakamakon gwajin Coronavirus da aka yi wa Lai Mohammed da Akeredolu ya fito

Sakamakon gwajin kwayar cutar Coronavirus da aka yi wa Gwamnan jihar Ondo, Mista Rotimi Akeredolu ya fito a ranar Alhamis inda ya nuna cewa gwamnan bai kamu da kwayar cutar ba.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Wahab Adegberno ya tabbatar wa The Punch wannan batun a wayar tarho.

Ya ce, "Sakamakon ya nuna cewa ba ya dauke da kwayar cutar. Ina tabbatar maka da hakan. Gwamnan kan shi a safiyar yau ya tabbatar da hakan.

Yanzu-yanzu: Sakamakon gwajin Coronavirus da aka yi wa Lai Mohammed da Akeredolu ya fito
Yanzu-yanzu: Sakamakon gwajin Coronavirus da aka yi wa Lai Mohammed da Akeredolu ya fito
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Rashin iya gamsar da matarsa a wurin kwanciya ya saka wani mutum kashe kansa

Kazalika, Ministan sadarwa da al'adu na kasa, Mista Lai Moihammed shi ma ya ce baya dauke da kwayar cutar.

Ministan ya ce an masa gwajin ne a ranar Laraba.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya ke amsa tambayoyi a kansa da kuma takwarorinsa yayin taron manema labarai bayan ganawar da suka yi a Abuja a ranar Alhamis.

A wani rahoton, kunji cewa gwamnatin tarayya ta ce ba gaskiya bane jita-jitar da ake yadawa na cewa an saka wa Shugaba Muhammadu Buhari na'urar taimakawa dan adam numfashi da ake kira Ventilator a turance.

Jita-jita na ta yawo a dandalin sada zumunta na cewa shugaban kasar ya kamu da kwayar cutar coronavirus.

Ministan sadarwa na kasa, Lai Mohammed ne ya yi wannan karin hasken yayin wata taron manema labarai da ya kira a birnin tarayya Abuja a yau.

Lai Mohammed ya jadadda cewa shugaban kasar lafiyansa kalau kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya kuma shawarci 'yan Najeriya su taimakawa hukumomi wurin ta hanyar sanar da hukuma idan suna daga cikin 'yan Najeriya da suka yi mu'amala da wadanda ke dauke da kwayar cutar musamman wadanda suka shigo jirgi suka dawo gida Najeriya daga kasashen waje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel