Matsalar tsaro: Ba zan sake sulhu da miyagun yan bindiga ba – Gwamnan Neja

Matsalar tsaro: Ba zan sake sulhu da miyagun yan bindiga ba – Gwamnan Neja

Gwamnatin jahar Neja ta bayyana cewa ba za ta sake tattaunawa da kungiyoyin yan bindiga da suka addabi al’ummar jahar ba, sai dai ya ce zasu bullo da sabbin hanyoyo da tsare tsare na kawo karshen yan bindigan.

Babban sakatariyar watsa labarai ta gwamnan jahar Abubakar Sani Bello, Mary Berje ce ta sanar da haka inda tace gwamnan ya bayyana haka ne yayin da mataimakin sufetan Yansanda, DIG Abdulmajid Ali da AIG Hosea Katma suka kai masa ziyara a ofishinsa.

KU KARANTA: Jerin manyan mutanen da suka yi cudanya da Abba Kyari kafin a tabbatar ya kamu da Coronavirus

Gwamna Bello ya bayyana damuwarsa da yadda yan bindiga suke kai hare hare babu kakkautawa tare da cin karensu babu babbaka a jahar, don haka yace lokaci da yayi da zasu yi fito na fito da yan bindigan.

Gwamnan ya bayyana harin da yan bindigan suka kai a kwana kwanan nan a kauyen Galadiman Kogo dake karamar hukumar Shiroro a matsayin abin takaici, kuma abin da ba zai iya lamunta ba, sa’annan yayi alkawarin hukunta duk wadanda suka kai harin.

“Muna aiki tare da gwamnonin jahohin Arewa maso yamma tare da hukumomin tsaro don gano inda yan bindigan suke fakewa da kuma sansanoninsu, nan bada jimawa ba zamu kai ma sansanoninsu hari.” Inji shi.

Daga karshe ya jajanta ma iyakan dakarun Sojin Najeriya da na jami’an Yansanda da aka kashe yayin da suke aikin tabbatar da tsaro a jahar, sa’annan yayi addu’ar Allah Ya jikansu.

A wani labarin kuma, Yayin da ake jimamin kamuwar gwamnan Bauchi, Bala Muhammad da annobar Coronavirus ba, kwatsam sai ga wasu gungun miyagu yan bindiga sun sace Yayansa, Yaya Adamu.

Yan bindiga sun yi awon gaba da Yaya Adamu ne a ranar Laraba, 25 g watan Maris da misalin karfe 7:30 na dare a gidansa dake Unguwan Jaki, cikin kwaryar garin Bauchi.

Wannan lamari ya faru ne bayan kimanin sa’o’i 72 da gwamnan jahar Bauchi, Bala Muhammad ya killace kansa daga cudanya da jama’a sakamakon mu’amalar da ya yi da wani mutumi dake dauke da cutar Coronavirus.

Daga bisani a ranar Talata aka tabbatar da gwamnan ya kamu da cutar, bayan sakamakon gwajin da jami’an hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC, suka gudanar a kansa ya tabbatar da hakan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel