Gwamnan jahar Akwa Ibom ya sanya dokar hana shiga da fita a jahar

Gwamnan jahar Akwa Ibom ya sanya dokar hana shiga da fita a jahar

Gwamnatin jahar Akwa Ibom ta dauki matakin kulle iyakokinta da makwabta jahohi tare da hana zirga zirgan ababen hawa daga shiga ko fita jahar har sai yadda hali ya yi sakamakon bullar cutar Coronavirus mai toshe numfashin dan Adam.

Premium Times ta ruwaito koda yake babu wani labarin bullar cutar a jahar, amma gwamnatin ta dauki matakin ne don kare yaduwarsa zuwa jahar, don haka ta umarci ma’aikata su koma zaman gida daga ranar 30 ga watan Maris.

KU KARANTA: Jerin manyan mutanen da suka yi cudanya da Abba Kyari kafin a tabbatar ya kamu da Coronavirus

Sakataren gwamnatin jahar, Emmanuel Ekwuem ne ya sanar da haka da safiyar Alhamis, 26 ga watan Maris, inda ya umarci jama’an jahar su yi zamansu a gida, sa’annan ya bayyana cewa gwamnati za ta hada hannu da Yansanda don tabbatar da dokar.

Mista Ekwuem ya kara da cewa kamfanin jirgin sama na jahar, Ibom Air zai dakatar da duk wani zirga zirgarsa daga ranar 29 ga watan Maris.

“Yayin da kowa zai cigaba da zama a gida tsawon mako daya, gwamnati za ta cigaba da bin diddigin yaduwar cutar don tabbatar da bata shigo jahar nan ba, don haka gwamnan jahar ya gargadi jama’a su kauce ma firgita jama’a ta hanyar watsa labaran kanzon kurege.” Inji shi.

A wani labari kuma, Majinyata shida da ke fama da cutar coronavirus a jihar Legas ne a yau suka warke. Za a sallamesu daga cibiyar killace majinyatan cutuka masu yaduwa da ke Yaba a jihar.

Tunde Ajayi, mai bada shawara ta musamman ga gwamnan jihar Legas, ya bayyana hakan a shafinsa na twitter a yau Alhamis. Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, ya rubuta:

"Shida daga cikin majinyatan cutar COVID-19 ne suka warke, kuma za a sallamesu nan ba da daewa ba. Abinda jihar Legas ke yi a yanzu ya sha banban. Mu ne a gaba."Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel