Coronavirus: Karya ne, ba a saka wa Buhari na'urar taimakawa numfashi ba - FG

Coronavirus: Karya ne, ba a saka wa Buhari na'urar taimakawa numfashi ba - FG

Gwamnatin Tarayya ta ce ba gaskiya bane jita-jitar da ake yadawa na cewa an saka wa Shugaba Muhammadu Buhari na'urar taimakawa dan adam numfashi da ake kira Ventilator a turance.

Jita-jita na ta yawo a dandalin sada zumunta na cewa shugaban kasar ya kamu da kwayar cutar coronavirus.

Ministan sadarwa na kasa, Lai Mohammed ne ya yi wannan karin hasken yayin wata taron manema labarai da ya kira a birnin tarayya Abuja a yau.

Lai Mohammed ya jadadda cewa shugaban kasar lafiyansa kalau kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Coronavirus: Karya ne, ba a saka wa Buhari na'urar taimakawa numfashi ba - FG

Coronavirus: Karya ne, ba a saka wa Buhari na'urar taimakawa numfashi ba - FG
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Rashin iya gamsar da matarsa a wurin kwanciya ya saka wani mutum kashe kansa

Ya ce, "Ina son yin magana game da labarun karya da ake yadawa game da coronavirus. Annobar labaran karya tana neman fin da annobar coronavirus hatsari kuma hakan cikas ne ga kokarin da muke yi na magance cutar.

"Wasu daga cikin labaran karyan sun hada da cewa; Na'urar taimakawa numfashi biyu kawai muke da shi a Abuja kuma an bawa wani babban jami'in gwamnati guda daya.

"Kuma wai akwai wani jirgin kasar Burtaniya da ya nufo Najeriya duk rufe filayen sauka da tashin jirage da aka yi tun ranar Laraba.

"Kuma wai Shugaba Muhammadu Buhari yana ta tari kuma a halin yanzu an saka masa na'urar taimakawa numfashi wato ventilator. Wannan dukkansu karya ne."

Minsitan ya ce ana can ana kokarin tuntubar 'yan Najeriya 4,370 da ake zargin sun yi cudanya da wanda ke dauke da cutar.

Ya bayyana fargabar cewa akwai yiwuwar adadin wadanda ke dauke da cutar zai karu muddin idan abin ya shiga cikin gari.

Ya kara da cewa, "muna da mutane 4,370 da muke kokarin tuntuba. Muna kira da duk wadanda suka yi mu'amala da wadanda ke da cutar su sanar da hukuma. Muna kira ga 'yan Najeriya su taimaka wa hukuma. Cutar na gab da yaduwa. Ya zama dole mu kare afkuwar hakan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel