Gwamnatin tarayya za ta baiwa NCDC N6.5bn domin yakar Coronavirus

Gwamnatin tarayya za ta baiwa NCDC N6.5bn domin yakar Coronavirus

Gwamnatin tarayya za ta saki kudi N6.5 billion ga cibiyar takaita yaduwar cututttuka a Najeriya NCDC, ministar kudi, Zainab Ahmed Shamsuna, ta laburta.

Ta bayyana hakan a zaman ganawa da shugabannin majalisar dattawa a Abuja ranar Laraba.

Ministar ta bayyana cewa za'a saki kudin ne matsayin tallafi wajen yakar yaduwar cutar Coronavirus a Najeriya.

Zainab Ahmed, gwamnan CBN, da wasu masu ruwa da tsaki a bangare kudi sun gana da yan majalisar ne domin tattauna irin shirin da suke yi wajen rage burin kasafin kudin 2020 sakamakon illar da Coronavirus ta yiwa farashin danyen mai a kasuwar duniya.

A jawabinta, ministar ta ce gwamnatin tarayya ta shirya bada tallafi ga bangaren kiwon lafiya ta hanyar cire haraji kan kayayyakin maganin da ake shigowa Najeriya.

Hakazalika gwamnatin tarayya za ta saki N6.5 billion amma sau biyu (N1.5 billion da N5 billion) ga cibiyar NCDC matsayin tallafi domin yakar yaduwar cutar Coronavirus a Najeriya.

Bugu da kari, gwamnatin jihar Legas za ta samu tallafin N10 billion domin yakar Coronavirus.

Ta sanar da yan majalisar cewa Najeriya ta samu tallafin $18.2 million daga hannun gwamnatin kasar Japan domin inganta cibiyoyin NCDC bakwai a fadin tarayya.

Gwamnatin tarayya za ta baiwa NCDC N6.5bn domin yakar Coronavirus

Zainab Ahmed
Source: UGC

A bangare guda, Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta yi gargadin cewa ba a amince da Chloroquine a matsayin maganin kwayar cutar Covid-19 da akafi sani da Coronavirus ba.

Shugaban hukumar Dakta Chikwe Ihekweazu ne ya bayar da wannan gargadin a Abuja a ranar Alhamis yayin da ya ke magana kan wasu rahotanni a kafafen yada labarai da ke nuna cewa mutane suna iya kare kansu daga kamuwa daga kwayar cutar ta hanyar amfani da Chloroquine ko amfani da shi wurin yi wa wanda suka kamu magani.

Ya ce, "Ya kamata 'yan Najeriya su tuna cewa Cibiyar Lafiya ta Duniya (WHO) ba ta amince da amfani Chloroquine da sauran danginsa ba wurin maganin coronavirus ba.

"Akwai alamun nasara wurin amfani da su amma kawo yanzu ba a amince da amfani da su ba domin maganin Covid-19."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel