Ba a tabbatar cewa Chloroquine na maganin Coronavirus ba - NCDC

Ba a tabbatar cewa Chloroquine na maganin Coronavirus ba - NCDC

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta yi gargadin cewa ba a amince da Chloroquine a matsayin maganin kwayar cutar Covid-19 da akafi sani da Coronavirus ba.

Shugaban hukumar Dakta Chikwe Ihekweazu ne ya bayar da wannan gargadin a Abuja a ranar Alhamis yayin da ya ke magana kan wasu rahotanni a kafafen yada labarai da ke nuna cewa mutane suna iya kare kansu daga kamuwa daga kwayar cutar ta hanyar amfani da Chloroquine ko amfani da shi wurin yi wa wanda suka kamu magani.

Ya ce, "Ya kamata 'yan Najeriya su tuna cewa Cibiyar Lafiya ta Duniya (WHO) ba ta amince da amfani Chloroquine da sauran danginsa ba wurin maganin coronavirus ba.

"Akwai alamun nasara wurin amfani da su amma kawo yanzu ba a amince da amfani da su ba domin maganin Covid-19.

Ba ta tabbatar cewa Chloroquine na maganin Coronavirus ba - NCDC

Ba ta tabbatar cewa Chloroquine na maganin Coronavirus ba - NCDC
Source: UGC

DUBA WANNAN: Rashin iya gamsar da matarsa a wurin kwanciya ya saka wani mutum kashe kansa

"Ya dace 'yan Najeriya su sani shan magunguna ba tare da likita ya rubuta wa mutum ba yana iya jefa rayuwar mutum cikin hatsari har ma ya mutu.

"Ku dena amfani da magunguna ta hanyar da ba su dace ba. Mun san cewa mutane suna cikin mawuyacin hali da damuwa amma ma'aikatar Lafiya da NCDC suna iya kokarinsu domin tabbatar da lafiyar dukkan 'yan Najeriya.

"Ba a tabbtar da Chloroquine da hydroxylchloroquine ba domin magance kwayar cutar Covid-19 da ciwuka masu alaka da ita."

Shugaban na NCDC ya ce har yanzu kwararru suna cigaba da gwaje-gwaje a Chloroquine da hydroxylchloroquine a matsayin maganin coronavirus.

Ya ce idan ba a tabbatar da ingancin amfani da shi da kuma abubuwan da maganin zai iya haifar wa a jikin mutum ba, bai dace a fara amfani da shi ba.

Tuni da NCDC ta fara wallafa sakonni na wayar da kan mutane a kan cutar da kuma karyata jita-jita da karerayi da wasu ke yadawa da ka iya jefa mutane cikin hatsari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel