An killace mutane 27 da suka yi cudanya da Gwamna Bala Muhammad dake dauke da Coronavirus

An killace mutane 27 da suka yi cudanya da Gwamna Bala Muhammad dake dauke da Coronavirus

Akalla mutane 27 ne suka bayyana kansu domin a killacesu bayan sun yi mu’amala da gwamnan jahar Bauchi, Sanata Bala Muhammad wanda hukumar NCDC dake yaki da yaduwar cututtuka ta bayyana ya kamu da cutar.

Sashin kula da yaduwar cututtuka na ma’aikatar gwamnatin jahar Bauchi ce ta tabbatar da haka inda tace a yanzu haka an kebance na kwanaki 14, kuma suna karkashin sa idon jami’an hukumar NCDC.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus: Dakarun Sojin Najeriya a shirye suke su garkame Najeriya

Punch ta ruwaito baya ga killacesu, NCDC ta dauki jininsu da yawunsu domin yi musu gwajin cutar Coronavirus, a yanzu haka suna jiran fitowar sakamakon gwajin.

Bugu da kari, rahotanni sun bayyana gwamnatin Bauchi ta samar da wuraren killace marasa lafiya a asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya dake Azare da kuma asibitin kwararru na Bauchi da babban asibitin Toro.

A hannu guda kuma mataimakin gwamnan jahar Bauchi, Sanata Baba Tela ya bada umarnin kulle dukkanin kasuwannin jahar, Tela ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake ganawa da manema labaru a fadar gwamnatin jahar.

“Amma dokar banda shagunan sayar da abinci, magani, gidajen burodi, gidajen mai da kuma shagunan da ake sayar da kayan amfani na yau da kullum, amma su ma dole ne sai sun bi umarnin jami’an kiwon lafiya don rage yaduwar cutar.” Inji shi.

Daga karshe, mataimakin gwamna Baba Tela yace Yansanda za su dabbaka umarnin gwamnati don ganin jama’a sun kiyaye dokokin da aka shimfida game da kare yaduwar cutar, kuma duk wanda aka kama da laifi zai fuskanci fushin hukuma.

A wani labarin kuma, kafatanin rundunonin Najeriya na zaune cikin shirin ko-ta-kwana tare da aiki da cikawa domin dabbaka umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na garkame Najeriya da zarar ya bayar da umarnin yin hakan sakamakon yaduwar annobar Coronavirus.

Wata majiya daga cikin manyan jami’an Sojin kasar nan ta shaida mata cewa an aika ma kowanne rukunin Sojin Najeriya sako daga shelkwatar tsaro ta kasa a kan su kasance cikin shirin ko-ta-kwana, a ranar Talata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel