COVID-19: Mazauna Legas na tururuwar siyan Dogonyaro da Tagairi a matsayin magani

COVID-19: Mazauna Legas na tururuwar siyan Dogonyaro da Tagairi a matsayin magani

- Kungiyar masu siyar da magungunan gargajiya ta jihar Legas ta bayyana yadda ake tururuwar siyan Tagairi da kuma ganyen dalbejiya wanda ake kira da Dogonyaro

- Modinat Fasuyi-Onike, shugabar kungiyar masu magungunan gargajiya da ke kasuwar Alade ta bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Legas

- Tayi kira ga 'yan Najeriya da su dakata har sai hukumomi sun tabbatar da maganin cutar kafin su fara danganta shi da maganin gargajiya

Kungiyar masu siyar da magungunan gargajiya ta jihar Legas ta bayyana yadda ake tururuwar siyan Tagairi da kuma ganyen dalbejiya wanda ake kira da Dogonyaro tun bayan barkewar cutar a kasar nan.

Modinat Fasuyi-Onije, shugabar kungiyar masu magungunan gargajiya da ke kasuwar Alade ta bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Legas a ranar Alhamis.

Fasuyi-Onike ta ce: "Jama'a ne ke sanar damu cewa wani ya wallafa yadda tagairi ke maganin cutar a kafar sada zumuntar zamani. Idan aka zuba shi a kasa, yana kashe kwayoyin cutar kyanda da makamancinsu.

"Haka kuma Dogonyaro yana kashe kwayoyin cutar zazzabin cizo sauro. A don haka ne mutane ke ta siya kuma ake ta nemanshi a kasuwanni.

COVID-19: Mazauna Legas na tururuwar siyan Dogonyaro da Tagairi a matsayin magani

COVID-19: Mazauna Legas na tururuwar siyan Dogonyaro da Tagairi a matsayin magani
Source: UGC

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: FG za ta haramta tafiye-tafiye tsakanin jiha da jiha

"Ina tunanin ana ci gaba da neman Dogonyaro ne saboda ana amfani dashi wajen maganin zazzabin cizon sauro a maimakon Chloroquine. Tunda kuwa ance a cikin alamun coronavirus akwai zazzabi mai zafi kamar na zazzabin cizon sauro, shiyasa jama'a ke neman Dogonyaro."

Ta sanar da Kamfanin dillancin Labaran Najeriya cewa bata goyon bayan amfani da magungunan gargajiya wajen maganin cutar tunda har yanzu masu bincike basu gano sahihin maganinsa ba.

Tayi kira ga 'yan Najeriya da su dakata har sai hukumomi sun tabbatar da maganin cutar kafin su fara danganta shi da maganin gargajiya.

Amma kuma ta ce babu wata illa da ganyen Dogonyaro yake da shi, ballantana wajen maganin zazzabin cizon sauro.

Fasuyi-Onike ta shawarci 'yan Najeriya da su mayar da hankali a kan shawarar da gwamnati ta bada na tsaftace kai da muhalli a matsayin hanyar hana yaduwar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel