Abubuwan da ya kamata ka sani game da Coronavirus a Najeriya

Abubuwan da ya kamata ka sani game da Coronavirus a Najeriya

Yau ana neman wata daya cir da shigowar cutar Coronavirus Najeriya. Legit.ng Hausa ta tattaro muku abubuwan da ya kamata ku sani game da cutar a kasar Najeriya.

1. An tabbatar da shigowarta Najeriya ranar 27 ga Febrairu a jihar Legas ta wani dan kasar Italiya ya kawo ziyarar aiki kamfanin siminti.

2. Kawo yanzu an tabbatar da mutane 51 sun kamu, biyu sun samu sauki kuma an sallamesu, daya ya mutu

3. Cibiyar gwaji biyar kadai ake da su a Najeriya (Legas 2, Abuja, Edo da Osun)

4. Ba'a amince asibitoci masu zaman kansu su gwada mutane ba

5. Manyan mutanen da suka kamu da cutar sun hada Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, Dan Atiku Abubakar, gwamnan jihar Bauchi, Bala AbdulKadir, kakakin majalisar dokokin jihar Edo.

6. An kulle fadar shugaban kasa bayan gwada shugaban kasa, Muhammadu Buhari; mataimakinsa Yemi Osinbajo; da iyalansu kuma an tabbatar bata harbesu ba

7. An hana zirga-zirga, hada-hada, kasuwanci (Illa kayan masarufi), sufuri (da sharruda) a jihohin Legas, Kaduna, Neja, Abuja Dss

8. An kulle dukkan makarantun sakandare da jami'o'i a fadin tarayya

9 An umurci dukkan ma'aikatan gwamnati daga daraja 1 zuwa 12 suyi zamansu a gida na tsawon makonni biyu

10. Shugaban Alkalan Najeriya, CJN Tanko Muhammad, ya bada umurnin kulle duka kotunan Najeriya

11. Cutar ta bulla a jihohi 9 (Lagos- 32, FCT- 10, Ogun- 3, Ekiti- 1, Oyo- 1, Edo- 1, Bauchi-1 Osun-1 Rivers-1)

12. An kulle Masallatai da Cocuna a birnin tarayya, Legas, Kwara, Ogun Dss

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel