Abinda ya hana Abba Kyari killace kansa bayan dawowa da kasar Jamus

Abinda ya hana Abba Kyari killace kansa bayan dawowa da kasar Jamus

Abba Kyari, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki killace kansa bayan ya dawo daga kasar Jamus da Ingila ne saboda a lokacin da ya dawo ba a samu barkewar cutar coronavirus ba a kasashen, kamar yadda wata majiya daga iyalansa ta tabbatar.

Wannan kuwa ya ci karo da yadda jama’a ke yada cewa ya ki killace kansa ne duk da kuwa cibiyar kula da yaduwar cutuka ta kasa ta bada shawarar ya killace kansa din.

Na hannun daman shugaban kasar, a ranar Litinin an gano cewa yana dauke da muguwar cutar coronavirus wacce ake tsammanin ya samu ne a yayin da ya kai ziyara kasar Jamus.

“Abba Kyari ya ziyarci kasar Jamus da Ingila daga ranar 8 zuwa 12 ga watan Maris. Ya iso Abuja a ranar 13 ga watan Maris. A wannan lokacin kuwa, daga kasar Jamus zuwa Ingila duka babu barkewar cutar wacce za ta sa ya killace kansa,” wani daga cikin iyalansa ya sanar yayin da ya bukaci a rufe sunansa.

Abinda ya hana Abba Kyari killace kansa bayan dawowa da kasar Jamus
Abinda ya hana Abba Kyari killace kansa bayan dawowa da kasar Jamus
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Bidiyon yadda wani sanata ya cire takunkumin hanci kafin yayi tari

A takaice dai, kasar Jamus da Ingila duk an samu barkewar cutar ne daga ranar 16 zuwa 17 ga watan Maris. Wannan duk bayan ya iso kasar Najeriya ne a ranar 13 ga watan Maris. Don haka bai take shawarar NCDC ba.

“Na san lokacin da Abba Kyari ya mika fasfotinsa ga ma’aikatar lafiya da kuma ta NCDC don tantancewa bayan ya dawo.” yace.

Wani daga cikin iyalansa, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya sanar da The Cable cewa koda aka killace shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar, yana cikin koshin lafiya.

“Ina gaisawa da Abba ta waya kuma yana cikin kwanciyar hankali. Ya damu matuka da sakonnin fatan alheri da masoya da abokan arziki ke tura masa.” Ya sanar da The Cable.

“Har a halin yanzu bai nuna wata alamar cutar ba bayan tarin da yake yi a wasu lokutan. Babu wani abu da ya wuce maganin tarin da yake yi wanda ake fama dashi. Babu zazzabi ko matsalar numfashi har yanzu.” Yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel