Gwamnan jahar Ondo ya killace kansa bayan mu’amala da gwamnan Bauchi
Gwamnan jahar Ondo, Rotimi Akeredolu ya shiga halwa inda ya kebance kansa domin kauce ma yada cutar Coronavirus wanda ake tunanin zai iya kamuwa da ita sakamakon mu’amalar da ya yi da gwamnan jahar Bauchi, Bala Muhammad.
Sahara Reporters ta ruwaito baya ga shiga halwa, gwamnan ya soke dukkanin sha’ani da suka shafe shin a tsawon kwanaki 14, wannan ya biyo bayan gwajin da aka yi ma Bala Muhammad, wanda sakamakon ya nuna Bala ya kamu da cutar.
KU KARANTA: Yadda babbar kasuwar Kaduna ta koma bayan dokar El-Rufai a kan Coronavirus
Wata majiya daga fadar gwamatin jahar ta bayyana cewa: “Gwamna Akeredolu yana Abuja a makon da ta gabata, inda ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da sauran gwamnonin APC, kuma a lokacin Coronavirus ta fara yaduwa.
“Don haka ya dauki matakin kandagarki bayan an sanar da sakamakon gwajin da aka yi ma gwamnan jahar Bauchi, dole tasa ya killace kansa saboda babu tabbacin ko ya kusanci Gwamna Bala Muhammad a Abuja ko akasin haka.” Inji shi.
Sai dai a daren Talata, gwamnan da kansa ta bakin mai magana da yawuns,a Donald Ojogo ya sanar da soke duk wasu sha’ani da suka shafe shi ko ofishinsa, haka zalika ya bayar da umarnin garkame dukkanin kasuwani don rage yaduwar cutar.
“A matakin farko, gwamnan ya bada umarnin rufe dukkanin kasuwanni na tsawo mako 1, illa shagunan sayar da abinci, magani da ruwa, haka zalika gwamnan ya dakatar da duk wasu tarukan siyasa a jahar, don haka gwamnan yake kira ga jama’a dasu bayar da hadin kai.” Inji shi.
A wani labarin kuma, wasu gungun yan bindiga sun kai farmaki a gidan shugaban kwamitin ko-ta-kwana dake yaki da yaduwar annobar nan mai toshe numfashi watau cutar Coronavirus na jahar Nassarawa, Dakta Ibrahim Adamu.
Yan fashin sun bi sawun Ibrahim, wanda shi ne daraktan kiwon lafiya a ma’aikatar kiwon lafiya ta jahar Nassarawa, yayin da yake kan hanyarsa ta komawa gida da misalin karfe 1:30 na dare.
Bayan sun kutsa kai cikin gidan nasa, yan fashin sun kwashe muhimman abubuwa da suka hada da kwamfutar Laptop, makullon motoci, katukan cire kudi da sauran kayayyaki mallakin matarsa.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng