Cutar #COVID19: Gwamnan jihar Neja ya killace kansa

Cutar #COVID19: Gwamnan jihar Neja ya killace kansa

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya killace kansa sakamakon halartan taron kungiyar gwamnonin Najeriya da aka gudanar ranar 18 ga Maris 2020.

Gwamnan ya bukaci killace kansa ne bayan daya daga cikin wadanda suka halarta taron, gwamnan Bauchi, Balam Mohammed, ya kamu da cutar.

Sakataren yada labaran gwamnan, Mary Noel Berje, ta bayyana hakan a jawabin da ta saki ranar Laraba.

Jawabin yace: "Dubi ga cewa a Abuja na kwashe makon da ya gabata domin halartan taron gwamnonin APC da shugaban kasa, taron gwamnonon Najeriya, taron majalisar tattalin arzikin tarayya da taron bankin duniya, ina ganin ya kamata a matsayin jagora in killace kaina har sai an gwada ni da iyali na."

"Hakazalika gwamna ya umurci dukkan hadimansa na kusa da mambobin majalisar zantarwarsa su killace kansu."

Game da lamarin sanya dokar ta baci a jihar, gwamnan ya yi kira da al'umma kada su tayar da hankulansu kan matakan da aka sa.

KU KARANTA: An haramtawa adaidaita sahu daukar fasinjoji, an saka wa masu mota sabuwar doka a Kaduna

Cutar #COVID19: Gwamnan jihar Neja ya killace kansa
Cutar #COVID19: Gwamnan jihar Neja ya killace kansa
Asali: UGC

A bangare guda, Sakamakon gwajin cutar COVID19 da shahrarren dan wasan kwaikwayon Kannywood da Nollywood, Ali Muhammad Nuhu, tare da Frodusa, Abubakar Bashir Maishadda, Dirakta Hassan Giggs da mawaki Ado Gwanja, ya fito.

A cewar Maishadda, dukkansu basu kamu da cutar kuma suna mika godiya ga masoya bisa addu'o'insu.

Za ku tuna cewa Ali Nuhu da wasu jaruman Kannywood sun halarci taron lambar yabon AMVCA a Legas inda kwamishanan kiwon lafiyan Legas, Farfesa Abayomi, ya bukaci dukkan wadanda suka halarci taron su gwada kansu saboda akwai yiwuwan sun kamu da Coronavirus.

Maishadda yace “Kowa zai iya kiran kansa abokinka amma baka sanin abokin kwarai sai lokacin kunci. Mun godewa addu'o'inku. Muna cikin koshin lafiya.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel