Da duminsa: Atiku ya yi alkawarin bada gudunmuwar N50m domin matsayin tallafi ga yan Najeriya

Da duminsa: Atiku ya yi alkawarin bada gudunmuwar N50m domin matsayin tallafi ga yan Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin bada gudunmuwar milyan hamsin cikin kudin tallafin da ake shirin baiwa yan Najeriya domin saukake radadin zaman gida sakamakon cutar Coronavirus.

Ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Laraba.

Ya ce zai bada gudunmuwar ne ta kamfaninsa Priam Group inda har gwamnatin tarayya ta shirya samar da tallafi ga yan Najeriya.

Yace: “Ina jinjinawa dukkan mutane da kamfanonin da suka taimakawa yan Najeriya yayin wannan annoba. Ina kara kira ga wasu kamfanonin da masu hannu da shuni su taimakawa mutane a irin wannan lokaci.“

“Priam Group ta yi alkawarin N50 million a madadina matsayin gudunmuwar tallafin da ya za a yiwa yan Najeriya.“

Za ku tuna cewa daya daga cikin yaran Atiku Abubakar ya kamu da cutar kuma ana jinyarsa a asibitin koyarwan jamiar Abuja dake Gwagwalada.

KU KARANTA Gwamnan Ekiti ya killace kansa bayan haduwa da mutane 2 masu cutar Coronavirus

Da duminsa: Atiku ya yi alkawarin bada gudunmuwar N50m domin yakar Coronavirus
Da duminsa: Atiku
Asali: Twitter

A bangare guda, Shugaban ma-aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, ya kamu da cutar Coronavirus sakamakon tafiyar da yayi zuwa kasar Jamus a makonni biyu da suka gabata.

Tuni an garzaya da shi Gwagwalada inda zai yi jinya.

Hakazalika gwamnan jihar Bauchi, Bala AbdulKadir Mohammed, ya kamu da cutar ta Coronavirus bayan zama tare da dan gidan Atiku Abubakar, a cikin jirgin saman Aero Contractors.

Bugu da kari, kakakin majalisar dokokin jihar Edi, Frank Okiye, ya zama mutum na farko da ya kamu da cutar Coronavirus a jihar Edo, mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu, ya laburta a Benin City.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng