Yanzu-yanzu: Kakakin majalisar dokokin jihar Edi ya kamu da Coronavirus

Yanzu-yanzu: Kakakin majalisar dokokin jihar Edi ya kamu da Coronavirus

Ta tabbata kakakin majalisar dokokin jihar Edi, Frank Okiye, ya zama mutum na farko da ya kamu da cutar Coronavirus a jihar Edo, mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu, ya laburta a Benin City.

Kakakin ya yi tafiya zuwa kasar Ingila kuma ya killace kansa daga dawowa a asibitin Irrua, dake karamar hukumar Esan na jihar.

Ya kara da cewa mutane biyu da ake zargin sun hadu da kaakakin sune matarsa da yarinyarsa kuma an gwada su, basu kamu ba.

Phiilip Shaibu yace “Ya tura samfurin jininsa kuma sakamakon shine ya kamu. Yana cikin koshin lafiya kuma sakamakon gwain da akayi iyalansa ya nuna cewa basu kamu ba.“

Yanzu-yanzu: Kakakin majalisar dokokin jihar Edi ya kamu da Coronavirus
Yanzu-yanzu: Kakakin majalisar dokokin jihar Edi ya kamu da Coronavirus
Asali: Facebook

Mun kawo muku rahoton cewa biyo bayan halartan taron kungiyar gwamnonin Najeriya da na tattalin arziki na kasa, Gwamna Godwin Obaseki ya shiga killace kansa.

A wani jawabi da aka saki a ranar Laraba, 25 ga watan Maris daga hadimin Obaseki, Crusoe Osagie, ya bayyana cewa Gwamna Bala Mohammed na Bauchi da Abba Kyari, Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wadanda ke dauke da cutar coronavirus duk sun halarci taron.

Sai dai kuma, Osagie bai fayyace cewar ko Obaseki ya fara ganin alamu na cutar ba, jaridar The Nation ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel