COVID-19: Jirgin sama daga Turai yana tunkaro Legas duk doka ta hana

COVID-19: Jirgin sama daga Turai yana tunkaro Legas duk doka ta hana

- Wasu ‘yan Najeriya sun nuna damuwarsu tare da tsoron saukar jirgin kamfanin British Airways da zai taso daga filin sauka da tashin jiragen sama na Hearthrow zuwa Legas

- Jirgin saman ana tsammanin zai sauka a jihar Legas ne duk da dokar haramcin saukar jiragen sama daga kasashen da cutar ta fi barkewa

- ‘Yan Najeriya sun gargadi gwamnatin tarayya a kan cewa za a iya fsukantar mummunan hatsari idan aka bar jirgin ya sauka a kasar nan

Wasu ‘yan Najeriya sun bayyana tsoronsu da firgici a kan yadda jirgin kamfanin British Airways zai baro filin sauka da tashin jiragen sama na Hearthrow zuwa Najeriya a yau Laraba, 25 ga watan Maris, duk da gwamnatin tarayya ta haramta saukar jirage daga kasashen da cutar ta barke.

Ingila na daya daga cikin kasashen da cutar coronavirus ta barke kuma rahoto ya nuna cewa ta kashe mutane har 340.

A bangare daya kuwa, Najeriya na kunshe da masu muguwar cutar har mutane 46 inda mutum daya ya riga mu gidan gaskiya.

Kamar yadda Legit.ng ta duba daga yanar gizon kamfanin British Airways, an bayyana lokacin tashi da saukar jirgin.

COVID-19: Jirgin sama daga Turai yana tunkaro Legas duk doka ta hana

COVID-19: Jirgin sama daga Turai yana tunkaro Legas duk doka ta hana
Source: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Osinbajo ya killace kansa bayan ya zauna kusa da Kyari a FEC

COVID-19: Jirgin sama daga Turai yana tunkaro Legas duk doka ta hana

COVID-19: Jirgin sama daga Turai yana tunkaro Legas duk doka ta hana
Source: UGC

Wasu ‘yan Najeriya da suka ga wannan jadawalin tashi da saukar jirgin sun nuna tsoro tare da kira ga gwamnatin Najeriya da ta duba hatsarin da hakan zai jawo.

A wani labari na daban, Bala Mohammed, gwamnan jihar Bauchi, ya bukaci jama'ar jiharsa da kada su ji tsoro a kan kebancesa da aka yi sakamakon cutar coronavirus da ya kamu da ita.

A ranar Talata ne dai aka tabbatar da cewa gwamnan na dauke da cutar coronavirus din. Mohammed ya killace kansa tun bayan da yayi hannu da dan Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, wanda aka gano yana dauke da cutar, kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa.

A sakon da gwamnan ya wallafa a shafinsa na twitter, Mohammed ya ce yana lafiya kuma har yanzu bai fara nuna wata alama ta cutar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel