Yanzu-yanzu: Prince Charles ya kamu da cutar COVID-19

Yanzu-yanzu: Prince Charles ya kamu da cutar COVID-19

- Prince Charles babban dan sarauniyar Ingila, Sarauniya Elizabeth II ya kamu da muguwar cutar coronavirus

- Prince Charles, babban dan sarauniyar Ingila kuma wanda ke jiran gadon sarautar Turai, ya kamu da cutar coronavirus kuma a halin yanzu yana killace a Scotland

- Matarsa, wacce ita ,ce gimbiyar Cornwall anyi mata gwajin amma ba ta dauke da cutar amma masana kiwon lafiya sun bukaci da ta kebance daga jama'a

Prince Charles babban dan sarauniyar Ingila, Sarauniya Elizabeth II ya kamu da muguwar cutar coronavirus.

Prince Charles, babban dan sarauniyar Ingila kuma wanda ke jiran gadon sarautar Turai, ya kamu da cutar coronavirus kuma a halin yanzu yana killace a Scotland.

Kamar yadda takardar da ta fito daga gidan Clarence ta bayyana:

“A halin yanzu yariman Wales ya kamu da muguwar cutar Coronavirus. Kananan alamun cutar sun fara bayyana a tare da shi amma a halin yanzu yana cikin koshin lafiya kuma yana ayyukansa daga gida a cikin kwanakin nan." cewar takardar

Yanzu-yanzu: Prince Charles ya kamu da cutar COVID-19
Yanzu-yanzu: Prince Charles ya kamu da cutar COVID-19
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Osinbajo ya killace kansa bayan ya zauna kusa da Kyari a FEC

“Matarsa, wacce ita ,ce gimbiyar Cornwall anyi mata gwajin amma ba ta dauke da cutar. Kamar yadda gwamnati da shawarar masana kiwon lafiya ta bayyana, yariman da gimbiyar suna killace ne a gida a Scotland. NHS a Aberdeenshire ne suka yi musu gwajin cutar." Ta kara da cewa.

Kamar yadda takardar ta bayyana, “Gano wajen wanda Yariman ya samo cutar a halin yanzu yana da wahala, ganin yadda ya dinga zirga-zarga tare da shiga jama’a a cikin makonnin da suka gabata.”

Fadar sarauniyar ta kara da cewa “Sarauniyar na cikin koshin lafiya.”

A wani labari na daban, darakta janar din NGF ya killace kansa tare da dukkan iyalansa sakamakon taron kungiyar gwamnonin Najeriya da ya halarta wanda Gwamnan Bauchi ya halarta.

Ya yi kira ga dukkan wadanda suka je taron da su bi ka'idar killace kansu tare da gaggauta sanar da NCDC wata alamar cutar idan suka gani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel