Da duminsa: Sakamakon gwajin Osinbajo ta fito, bai kamu da Coronavirus ba

Da duminsa: Sakamakon gwajin Osinbajo ta fito, bai kamu da Coronavirus ba

Sakamakon gwajin cutar Coronavirus da aka yiwa mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ta fito a ranar Laraba, 25 ga Maris, 2020.

Sakamakon ya nuna cewa bai kamu da cutar ba.

An bayyana sakamakon mataimakin shugaban kasan bayan awa 24 da ya killace kansa sakamakon zaman da yayi da shugaban ma-aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, wanda aka tabbatar ya kamu da cutar.

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan lamuran siyasa, Sanata Babafemi Ojudu ya alanta hakan a shafinsa na Tuwita inda yace:

“Sakamakon gwajin mataimakin shugaban kasa ya nuna bai kamu ba“

Da duminsa: Sakamakon gwajin Osinbajo ta fito, bai kamu da Coronavirus ba
Da duminsa: Sakamakon gwajin Osinbajo ta fito, bai kamu da Coronavirus ba
Asali: Twitter

Ga jerin wuraren da Abba Kyari ya ziyarta tun bayan dawowarsa Najeriya

Da farko dai Abba Kyari ya halarci daurin auren ‘Ya ‘yan Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, inda ya hadu da irinsu Aliko Dangote da manyan masu masu iko.

Haka zalika bayan nan Kyari ya halarci taron gwamnonin APC da aka yi a Ranar 16 ga Watan Maris tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa.

Gwamnoni 16 su ka halarci wannan taro sun hada: Gana Zulum, Jide Sanwo Olu, Dapo Abiodun, Godwin Obaseki, Atiku Bagudu, Abubakar Badaru da Aminu Masari.

Sauran Gwamnonin su ne Abdulrahman Abdulrazaq, Abdullahi Sule, Mohammed Sani, Simon Lalong da kuma Rotimi Akeredolu, Abdullahi Ganduje da Inuwa Yahya.

Har ila yau a wannan taro, Hadimin shugaban kasa Malam Abba Kyari ya hadu da sauran gwamnonin APC da su ka hada da Adegboyega Oyetola, Hope Uzodinma.

Kafin nan kuma Abba Kyari ya gana da shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole. Kashegari watau 17 ga Watan Maris, Kyari ya ja tawaga zuwa jihar Kogi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel